Shugaba Tinubu Zai Sake Shillawa Kasar Waje Awanni Kaɗan Bayan Ya Dawo Najeriya

Shugaba Tinubu Zai Sake Shillawa Kasar Waje Awanni Kaɗan Bayan Ya Dawo Najeriya

  • Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu zai kama hanya ya koma ƙasar Faransa awanni kaɗan bayan ya dawo Najeriya ranar Jumu'a
  • Bayanai sun nuna Tinubu ya katse ziyarar da yake yi a Faransa domin ya dawo ya rantsar da sabuwar shugabar Alkalan Najeriya ta riko
  • Sai dai bayan kammala bikin rantsar da Kudirat Kekere-Ekun, ana tsammanin Tinubu zai koma ya ƙarasa ziyararsa a kasar Faransa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Ana sa ran a yau Juma’a 23 ga watan Agustan 2024 shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai koma kasar Faransa sa'oi kaɗan bayan ya dawo Najeriya.

Shugaban ƙasar ya shigo Najeriya ne yau Jumu'a da safe daga ƙasar Faransa domin shaida sauyin da aka samu a ɓangaren shari'a bayan Alkalin Alkalai ya yi ritaya.

Kara karanta wannan

Magana ta ƙare, kotun koli ta yanke hukunci kan sahihancin zaɓen gwamnan APC

Shugaba Bola Tinubu.
Shugaba Tinubu Zlzai koma Faransa awanni bayan rantsar da sabuwar CJN Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Bola Tinubu ya rantsar da sabuwar CJN

Jim kaɗan bayan ya sauka, Tinubu ya jagoranci rantsar da mai shari’a Kudirat Kekere-Ekun a matsayin sabuwar Alkalin Alkalan Najeriya (CJN), Tribune Online ta tattaro labarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sabuwar shugabar alkalan Najeriya ta karɓi rantsuwar kama aiki da misalin ƙarfe 11:38 na safe a fadar shugaban ƙasa da ke birnin tarayya Abuja.

Mai shari’a Kudirat ta zama mace ta biyu a tarihi da ta rike wannan matsayi mai daraja bayan Mai shari’a Aloma Mariam Mukhtar, wacce ta zama CJN daga Yuli, 2012 zuwa Nuwamba 2014.

Mai shari’a Kudirar Kekere-Ekun za ta yi aiki a matsayin mukaddashin Alkalin Alƙalan Najeriya CJN har sai majalisar dattawa ta tabbatar da nadin ta.

Kusoshin gwamnati sun halarci rantsar da CJN

Bikin rantsarwar ya samu halartar manya da suka hada da alkalan kotun koli, shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio da Gwamna Babajide Sanwo-Olu na Legas.

Kara karanta wannan

Kekere Ekun: Abubuwa 4 da muka sani game da sabuwar shugabar alkalan Najeriya

Sauran sun hada da sakataren gwamnatin tarayya, George Akume, mai bada shawara tsaro Nuhu Ribadu, shugaban ma’aikatan Tinubu, Femi Gbajabiamila, da ministan yada labarai Mohammed Idris.

Shugaba Bola Tinubu zai koma Faransa

Shugaba Tinubu dai ya katse ziyarar da yake yi a kasar Faransa domin dawowa Najeriya ya rantsar da sabuwar CJN.

Kuma ana san shugaba ƙasar zai koma ƙasar Faransa da ke nahiyar Turai a yammcin yau Jumu'a domin ƙarasa abubuwan da suka kai shi.

Abubuwa 4 game da sabuwar CJN

A halin yanzu dai kallo ya koma kan Mai shari'a Kudirat Kekere-Ekun, wacce aka rantsar a matsayin shugabar alkalan Najeriya ranar Jumu'a.

Mun tattaro wasu muhimman abubuwa huɗu da ya kamata ku sani game da sabuwar CJN da ta kama aiki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262