Najeriya Ta Yi Rashi, Tsohon Shugaban ICPC Ta Ƙasa Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Najeriya Ta Yi Rashi, Tsohon Shugaban ICPC Ta Ƙasa Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • GTsohon shugaban hukumar ICPC, Emmanuel Ayoola ya riga mu gidan gaskiya ranar Talata, 20 ga watan Agusta, 2024
  • Iyalan marigayin ne suka tabbatar da hakan a wata sanarwa da suka fitar ranar Laraba, sun ce ya rasu ne yana da shekara 90 a duniya
  • Shugaban APC, Dr Musa Aliyu (SAN) ya aika saƙon ta'aziyya a madadin hukumar, ya ce ba za a taɓa mantawa da shi ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ICPC ta ƙasa, Mai shari’a Emmanuel Ayoola (Mai ritaya) ya riga mu gidan gaskiya.

Bayanai sun nuna cewa Ayoola ya rasu ne ranar Talata, 20 ga watan Agusta, 2024 yana da shekara 90 a duniya.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya faɗi gaskiya kan jita jitar yana shirin sauya sheƙa

Marigayi Emmanuel Ayoola.
Allah ya yiwa tsohon shugaban hukumar ICPC, Emmanuel Ayoola rasuwa Hoto: Emmanuel Ayoola
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta tattaro cewa hakan na kunshe ne a wata sanarwa da iyalan mamacin suka sanyawa hannu ranar Laraba, 21 ga watan Yuli, 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce:

"Cikin kankan da kai da miƙa godiya ga Allah, muna sanar da rasuwar babanmu, kakanmu kuma abin alfahari masoyinmu, Mai Shari'a Emmanuel Olayinka Ayoola (CON) mai ritaya."

Hukumar ICPC ta aika saƙon ta'aziyya

Shugaban ICPC na yanzu, Dr Musa Aliyu (SAN), ya aika sakon ta'aziyya ga iyalan tsohon shugaban hukumar, Mai shari’a Emmanuel Ayoola mai ritaya.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, Musa Aliyu ya ce ayyukan alherin da marigayin ya yi za su ci gaba da haskawa hukumar hanya a yaƙi da cin hanci.

Ya ƙara da cewa rayuwar Ayoola cike take da abubuwan koyi kuma ba za a taɓa mantawa da kyawawan ayyukansa ba.

Kara karanta wannan

"Ba zai iya ba," Malami ya buƙaci Shugaba Tinubu ya tsige Minista 1 nan take

"ICPC da ma kasa baki ɗaya mun yi rashin dattijo. Duk da haka, ayyukan da ya yi za su ci gaba da zaburar da mu a ƙoƙarinmu na yaƙi da cin hanci da rashawa."

Ayoola, tsohon alƙalin kotun koli wanda ya yi ritaya, ya riƙe shugaban ICPC tsakanin 2005 zuwa 2010, jaridar Leadership ta tattaro.

Mutum 4 sun mutu a haɗari a Kano

A wani rahoton, kwale-kwale da ya ɗauko mutane sama da 10 ya gamu da hatsari a kauyen Kauran Mata da ke karamar hukumar Madobi a Kano.

Rahotanni sun nuna cewa mutum huɗu daga ciki sun mutu, kana an ceto wasu mutum biyar da ransu kawo yanzu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262