Gwamna Ya Bayyana Gaskiya kan Jita Jitar Yana Shirin Sauya Sheƙa Daga PDP

Gwamna Ya Bayyana Gaskiya kan Jita Jitar Yana Shirin Sauya Sheƙa Daga PDP

  • Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas ya tabbatar da cewa yana nan daram a matsayin ɗan jam'iyyar PDP kuma ba shi da shirin sauya sheka
  • Fubara ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi bakuncin tawagar kwamitin amintattun PDP karkashin jagorancin Adolphus Wabara
  • Wannan dai na zuwa ne a lokacin da ake yaɗa jita-jitar gwamnan na shirin sauya sheƙa daga PDP saboda rigingimun da suka addabe ta a Ribas

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Sir Siminalayi Fubara ya bayyana cewa yana nan daram a matsayin ɗan jam'iyyar PDP.

Fubara ya faɗi hakan ne a Fatakwal, babban birnin Ribas, ranar Talata lokacin da ya karbi bakuncin ƴan kwamitin amintattu na PDP (BoT) a gidan gwamnatinsa.

Kara karanta wannan

Wani shugaban INEC ya yanke jiki ya faɗi, ya mutu bayan fitowa daga taro

Gwamna Fubara na jihar Ribas.
Gwamna Fubara ya musanta jita jita, ya ce yana nan daram a PDP Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Shugaban kwamitin amintattun PDP, Adolphus Wabara ne ya jagoranci mambobin BoT suka kai wa gwamnan ziyara, kamar yadda The Cable ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake jawabi, Gwamna Fubara ya ce ziyarar BoT kaɗai ta isa ƙaryata masu yaɗa jita-jitar yana shirin jefar da jam'iyyar PDP.

Gwamna Fubara na shirin barin PDP?

Gwamna Fubara ya ce:

“Ina matuƙar gode muku da kuka dauki duk wata kasada kuka tako zuwa jihar Ribas domin ganin gwamna da magoya bayan jam’iyyarmu. Mu nan ƴaƴan PDP ne babu surki.
"Ina cikin farin ciki da na ganku tare da mu yau domin tattauna abin da ya shafi Ribas, ina tabbatar maku cewa zama darma a PDP,
"Maƙasuɗin wannan ziyarar daya ce: mecece matsalar, ta yaya aka fara, ko kuma in ce me ya kawo ta kuma ta yaya ta koma yadda take a yau? Zan muku bayani idan mun shiga ganawar sirri."

Kara karanta wannan

Ganduje ya yi maganar neman takarar shugaban ƙasa a 2027, ya zargi ƴan Kwankwasiyya

Shugaban BoT ya faɗi dalilin zuwansu Ribas

A nasa jawabin, Wabara ya bayyana cewa uwar PDP ta ƙasa ta damu da halin da jam'iyyar ta shiga a jihar Ribas, ya ƙara da cewa sun zo ne domin sasanci da haɗin kai.

Mu, shugabannin wannan jam’iyya, mun zo nan ne domin neman zaman lafiya da hadin kai a jam’iyyar PDP," in ji shugaban BoT, The Sun ta rahoto.

Gwamnatin Tinubu ta kafa kwamiti

A wani rahoton na daban gwamnatin tarayya ta rantsar da kwamitin mutum 10 wanda zai sa ido da tabbatar da an aiwatar da hukuncin ƴancin ƙananan hukumomi

Sakataren gwamnatin, George Akume, shi ne zai jagoranci kwamitin wanda ya ƙunshi ministoci, gwamnan CBN da gwamnonin jihohi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262