Daga Karin Kumallo, Uwa da Yaƴanta 3 Sun Rasu a Wani Yanayi Mai Ban Tausayi
- Mahaifiya da yaranta uku sun mutu bayan karin kumallo da shinkafa da ake zargin an zuba guba a Ilorin, babban birnin Kwara
- Rahotanni sun bayyana cewa yanzu haka magidancin na kwance a asibiti ana kula da lafiyarsa saboda shi ma ya ci shinkafar
- Tuni dai aka yiwa waɗanda ibtila'in ya rutsa da su Sallar janaza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ilorin, jihar Kwara - Mutum huɗu ƴan gida ɗaya da suka haɗa da uwa da yara uku sun mutu bayan sun ci shinkafa a Ilọrin babban birnin jihar Kwara.
Lamarin ya faru ne a unguwar Oshin da ke kan titin Asa Dam a ranar Asabar da ta gabata, 17 ga watan Agusta, 2024.
Kamar yadda Daily Trust ta tattaro, ana zargin iyalan sun mutu ne sakamakon cin guba a wannam shinkafar da suka ci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwara: An yiwa mamatan janaza
A halin yanzu dai an yiwa mamatan jana'iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
An bayyana sunayen yaran da suka mutu da Abibat yar shekara 9, Zainab yar shekara bakwai da kuma Abdulfatai ɗan kimanin shekara biyar a duniya.
Yadda lamarin ya faru daga karin kumallo
Wata majiya ta ce iyalan sun yi karin kumallo da shinkafa gabanin su fita wurin neman halak da safiyar ranar Asabar.
"Bayan sun dawo da yamma, uwar ta fara shirin ɗora girki, ta zo tashin budurwar ƴarta da ke bacci, ta lura kumfa na fita a bakinta, aka nufi asibitin koyarwa UITH da ita, likitoci suka tabbatar rai ya yi halinsa.
"Sun dawo da gawar ɗiyar kenan suka taras sauran yaƴansu biyu sun fara nuna alamu, nan suka ɗauke su zuwa asibitin. Washe garin Lahadi uwar ta fara amai, ita ma aka kai ta asibiti
"Da sanyin safiyar yau Litinin likitoci suka tabbatar da uwar da yaran biyu duk sun mutu. Mai gidan da ya rage yanzu haka yana kwance a asibiti saboda shi ma ya ci abincin," in ji majiyar.
Yan sanda sun gayyaci shugaban NLC
Kuna da labarin Rundunar ƴan sanda ta gayyaci shugaban kungiyar kwadago NLC, Kwamared Joe Ajaero kan zargin hannu a ayyukan ta'addanci.
A wata sanarwa da ta fito daga sashen leken asiri na rundunar, ta buƙaci Ajaero ya kai kansa ranar Talata da misalin karfe 10:00 na safe.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng