NAHCON: Bola Tinubu Ya Naɗa Shugaban Izala a Muƙamin Gwamnatin Tarayya
- Bola Ahmed Tinubu ya naɗa shugaban Izala reshen Kano, Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan a matsayin sabon shugaban hukumar alhazai
- Shugaban ƙasar ya yi wannan naɗi ne bayan ya tsige Jalal Arabi, wanda EFCC ke bincika kan zargin karkatar da kuɗin tallafin hajjin bana 2024
- Mai magana da yuwun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar da yammacin yau Litinin
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya nada Sheikh Farfesa Abdullahi Saleh Usman (Pakistan) a matsayin Shugaban Hukumar Alhazai ta kasa (NAHCON).
Hakan na zuwa ne bayan shugaban ƙasar ta sauke Jalal Ahmad Arabi daga matsayin shugaban NAHCON kan badaƙalar tallafin hajjin 2024.
Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale ne ya sanar da naɗin Sheikh Pakistan a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Taƙaitaccen bayani kan Sheikh Pakistan
Farfesa Saleh Pakistan, fitaccen malamin Sunnah a Najeriya ya yi karatu a Jami’ar Madina da ke ƙasa mai tsarki da Jami’ar Peshawar da ke Pakistan.
Malamin yana da kwarewa a harkokin da suka shafi aikin Hajji kasancewar ya jagoranci hukumar jin daɗin alhazai ta jihar Kano a baya.
Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan shi ne shugaban ƙungiyar addinin Musulunci JIBWIS da aka fi sani da Izala ta reshen jihar Kano.
Bola Tinubu ya aikawa Pakistan sako
A sanarwar da Ngelale ya fitar, Shugaba Tinubu ya buƙaci Sheikh Pakistan ya yi ƙoƙarin sauke nauyin da Allah ya ɗora masa a wannna muƙami cikin gaskiya da rikon amana.
“Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin Farfesa Abdullahi Saleh Usman a matsayin shugaban hukumar alhazai ta kasa NAHCON.
"Farfesa Abdullahi, babban malami ne wanda ya yi karatu makarantun Musulunci, Jami'ar Madinah da Jami'ar Peshawar ta Pakistan," in ji sanarwar.
NAHCON ta kama jigilar alhazai
A wani rahoton kuma Hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta kawo ƙarshen aikin jigilar Alhazan Najeriya daga ƙasa mai tsarki zuwa gida.
Jirgin ƙarshe wanda yake ɗauke da Alhazan jihar Kwara ya baro ƙasa mai tsarki a ranar Talata, 16 ga watan Yulin 2024.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng