Mutum 2 Ƴan Gida Sun Mutu a Wani Mummunan Ibtila'i da Ya Rutsa da Su a Arewa

Mutum 2 Ƴan Gida Sun Mutu a Wani Mummunan Ibtila'i da Ya Rutsa da Su a Arewa

  • Matasa ƴan gida ɗaya sun mutu da ƙasa ta rufta masu a ramin haƙar ma'adanai a kauyen Kakaki a jihar Neja
  • Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin jihar Neja ta tura wakilai zuwa garin domin yiwa ƴan uwansu ta'aziyya
  • Babban sakataren ma'aikatar ma'danai a jihar Neja ya ce dokar dakstar da haƙar ma'adanai na nan daram

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Niger - Rahotanni sun nuna cewa mutum biyu ƴan gida ɗaya sun mutu sakamakon ruftawar ramin haƙar ma'adanai a kauyen Kakaki da ke jihar Neja.

Ibtila'in ya rutsa da ƴan uwan juna, Zubairu Ibrahim da Sadiq Ibrahim a ƙarshen makon nan a kauyen Kakaki da ke karamar hukumar Paikoro.

Taswirar jihar Niger.
Ramin hakar ma'adanai ya rufta kan wasu yan gida ɗaya a jihar Neja Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Wannan Lamari na zuwa ne bayan ruftawar ramukan haƙar ma’adanai uku da da suka afku a yankin ƙananan hukumomin Shiroro da Paikoro a watannin baya-bayan nan.

Kara karanta wannan

Matsala ta tunkaro Tinubu yayin da shirye shiryen sabuwar zanga zanga suka yi nisa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ƙasa ta danne mutum 2 a Niger

The Nation ta ruwaito cewa matasan biyu ƴan gida ɗaya sun bar gida ba tare da faɗawa iyayensu cewa za su je haƙar ma'adanai ba.

Sai da Magariba aka fahimci ba su dawo gida ba saboda ba a gansu a Masallaci ba kuma ba su ci abincinsu na dare ba.

Mutuwar ta girgiza mahaifinsu

Mahaifinsu Mallam Ibrahim ya bayyana cewa da farko sun yi tunanin sun fita yawo da abokai ne amma daga baya suka gano yaran sun tafi wurin haƙar ma'adanai.

Magidancin ya ƙara da cewa daga nan ne mutane garin suka fita nemansu, kuma abin takaici sai gawarwakinsu aka tsinta a ƙarƙashin kasar da ta rufta masu.

Mallam Ibramin ya ce lamarin ya girgiza shi matuƙa kuma yana tunanin yadda rayuwa za ta yi da shi bayan rasuwar matasan ƴaƴansa biyu.

Kara karanta wannan

'Yan bindigar da suka sace ɗaliban jami'o'i 2 a Arewa sun turo saƙo, sun faɗi buƙatarsu

Gwammatin Neja ta yi ta'aziyya

Tawagar ma'aikatar ma'adanai ta jihar Neja karkashin jagoranci babban sakatare Alhaji Yunusa Mohammed Nahauni sun kai ziyarar ta'aziyya bisa faruwar lamarin.

Babban Sakataren ya ce rashin bin umarnin Gwamna Muhammad Umar Bago na haramta haƙar ma'adanai ne ya jawo wannan ibtila'in.

Ya jaddada cewa har yanzu umarnin dakatar da hakar ma’adanai a jihar Neja yana nan daram kuma ma'aikatar za ta ci gaba da ƙoƙarin daƙile haƙar ma'adanai ba bisa ƙa'ida.

Ƴan bindiga sun kwace gonaki a Niger

A wani rahoton kun ji cewa mazauna kauyen Allawa da ke karamar hukumar Shiroro, jihar Neja sun yi wani yunkuri na komawa muhallansu bayan watanni biyar

Sai dai wasu da aka tura domin duba halin da garin ke ciki, sun ce 'yan bindiga sun kwace gidajen tare da kuma yin shuka a gonakinsu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: