Akpabio Ya Bayyana Mutuwar Sanatan da Ta Yi Matukar Girgiza Shi

Akpabio Ya Bayyana Mutuwar Sanatan da Ta Yi Matukar Girgiza Shi

  • Shugaban majalisar dattawa, sanata Godswill Akpabio ya je ta'aziyya ga iyalan marigayi sanata Patrick Ifeanyi Ubah
  • Akpabio ya bayyana mutuwar sanatan a matsayin abin da ya girgiza shi matuƙa saboda bai yi tsammanin cewa Ubah zai bar duniya a wannan lokacin ba
  • Shugaban majalisar dattawan ya ba su tabbacin cewa za a yiwa marigayin jana'iza wacce ta dace da shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Legas - Shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio ya jagoranci tawagar sanatoci domin yin ta’aziyya ga iyalan marigayi Sanata Ifeanyi Ubah.

Akpabio da sauran sanatocin sun je ta'aziyyar ne a gidan marigayin da ke Legas a ranar Asabar.

Akpabio ya yi ta'aziyyar Ifeanyi Ubah
Akpabio ya girgiza saboda mutuwar Ifeanyi Ubah Hoto: Nigerian Senate, Senator Dr. Patrick Ifeanyi Ubah
Asali: Facebook

Akpabio ya girgiza da mutuwar Ifeanyi Ubah

Wata sanarwa da mataimaki na musamman kan harkokin yaɗa labarai na shugaban majalisar dattijawan, Jackson Udom, ya fitar ta tabbatar da hakan, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fara daukar matakin tsuke bakin aljihun gwamnati

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Godswill Akpabio ya bayyana cewa mutuwar sanatan ta yi matuƙar girgiza shi.

"Na girgiza matuƙa lokacin da na samu labarin. Ba mu taɓa tsammanin wannan rashin ba, haƙiƙa na girgiza matuƙa."

- Godswill Akpabio

Akpabio ya bayyana sanata Ifeanyi Ubah a matsayin ginshiƙi a cikin majalisar dattawa ta 10 inda ya yaba kan jajircewarsa da kishin ƙasarsa, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

Akpabio ya yi ta'aziyya ga iyalan sanatan

Da yake yiwa matarsa da ƴaƴansa ta'aziyya, ya buƙace su da ɗauki dangana kan wannan rashin da suka yi.

Shugaban majalisar dattawan ya ba su tabbacin cewa zai ba su dukkanin taimakon da ya dace domin ganin an yi masa jana'izar da ta dace da shi.

Da yake magana a madadin iyalan, Prince Chidi Orizu, ya nuna matuƙar godiyarsa kan ziyarar tare da yin alƙawarin sanar da majalisar duk halin da ake ciki kan shirin binne marigayin.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban INEC ya yi babban rashi da mahaifiyarsa ta rasu a Abuja

Sanatocin da suka yiwa shugaban majalisar rakiya sun haɗa da Osita Ngwu, Saliu Mustapha, Sunday Karimi da Adetokunbo Abiru.

Sanata Ifeanyi Ubah, wanda ya wakilci Anambra ta Kudu, ya rasu ne a ranar, 27 ga watan Yulin 2024 a birnin Landan.

Tinubu ya yi ta'aziyyar Ifeanyi Ubah

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya tura saƙo ga iyalan Sanata Ifeanyi Ubah bayan sanar da mutuwars a birnin Landan.

Shugaba Bola Tinubu ya kuma tura saƙon ta'aziyya ga ƴan uwa da abokan marigayin inda ya ce tabbas rashin na sa babban abin takaici ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng