Gwamna Ya Yi Muhimmin Abin Alheri Yayin da Jirgi Ya Halaka Bayin Allah a Arewa
- Gwamnan jihar Sakkwato Ahmed Aliyu ya ware tallafin N30m ga waɗanda hatsarin jirgin ruwa ya rutsa da su a kauyen Dundaye
- Gwamnan ya ce gwamnatinsa za ta bai wa iyalan mutum biyar da suka rasu a haɗarin N15m yayin da waɗanda suka tsira kuma za a ba su N15m
- Ya ce zai samar da jiragen ruwa na zamani da rigunan ruwa domin kare rayukan al'umma a lokacin da suke tafiya a ruwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Jigawa - Gwamna Ahmed Aliyu na Sokoto ya bayar da gudunmawar kudi N30m ga iyalan wadanda hatsarin jirgin ruwa ya rutsa da su a ƙauyen Dundaye.
Idan baku manta ba a ƙarshen makon da ya gabata, wani kwale-kwale ya kife a kauyen Dundaye da ke karamar hukumar Wamakko a jihar Sakkwato.
Rahoton Tribune Nigeria ya nuna cewa haɗarin jirgin ya laƙume rayukan mutum biyar, yayin da sauran kuma aka samu nasarar ceto su da rai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Aliyu ya ba da kyautar N30m
Da yake sanar da bayar da tallafin, Gwamna Aliyu ya ce gwamnatinsa za ta ba iyalan waɗanda Allah ya yiwa rasuwa a hatsarin N15m
Gwamnan ya ƙara da cewa waɗanda Allah ya yiwa gyaɗar dogo suka tsira daga haɗarin, za su samu N15m, jimulla N30m kenan.
Gwamnatin Sokoto za ta sayo jiragen zamani
Ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar za ta samar da jiragen ruwa na zamani da rigunan ruwa domin tabbatar da kariya ga al'umma idan suka shiga ruwan.
Ahmed Aliyu ya ce:
"Ina ƙara kashedi ga masu jirgin ruwa su daina sakaci a lokacin da suka ɗauko mutane, na samu labarin gangancin direba ne ya jawo haɗarin, don Allah ku daina."
Ahmed Aliyu ya ba mazauna shawara
Gwamna Aliyu ya buƙaci mutanen da ke rayuwa a kewayen tafkin ɗa su yi amfani da damar wajen yin noman rani da sauran ayyukan noma da ruwan.
A cewar gwamnan, hakan zai taimaka wajen samar da isasshen abinci a jihar Sakkwato da ma ƙaa baki ɗaya.
Jigawa ta fara rabon tallafin Tinubu
Kun ji cewa Gwamna Umar Namadi ya kaddamar da fara rabon tallafin buhunan shinkafa, masara, dawa da gero ga masu ƙaramin ƙarfi a Jigawa.
Gwamnan ya bayyana cewa za a raba tallafin a dukkan gundumomi 187 da ke ƙananan hukumomi 27 a jihar.
Asali: Legit.ng