Gwamna Ya Cika Alkawari, Ya Fara Rabawa Talakawa Tallafin Buhunan Shinkafa da Masara
- Gwamna Umar Namadi ya kaddamar da fara rabon tallafin buhunan shinkafa, masara, dawa da gero ga masu ƙaramin ƙarfi a Jigawa
- Gwamnan ya bayyana cewa za a raba tallafin a dukkan gundumomi 187 da ke ƙananan hukumomi 27 a jihar
- Da yake jawabi a wurin taron kaddamarwa, gwamnan ya ce kayan tallafin sun fito ne daga gwamnatin tarayya don a rabawa mabukata
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Jigawa - Gwamnatin jihar Jigawa ta kaddamar da rabon buhunan shinkafa 59,000 mai nauyin kilogiram 25 da hatsi iri-iri ga marasa galihu a faɗin jihar.
Gwamnatin jihar ta fara rabon waɗannan kayayyakin abinci ga maɓukata da marasa galihu a gundumomi 287 da ke ƙananan hukumomi 27 a Jigawa.
Gwamna Umar Namadi Ɗanmodi ne ya jagoranci ƙaddamar da fara rabon tallafin abincin a gidan gwamnati da ke birnin Dutse, kamar yadda Leadership ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Tinubu ta kai tallafi Jigawa
Da yake jawabi a wurin taron, Gwamnan Namadi ya ce gwamnatin tarayya karƙashin Bola Ahmed Tinubu ce ta turo kayan abincin don a rabawa jama'a.
Ya ce kayayyakin abincin da za a raba sun hada da buhunan dawa 13,825, buhunan gero 9,500, buhunan masara 11,500 da buhunan shinkafa 24,000.
Umar Namadi ya ce:
“Domin tabbatar da tallafin ya shiga gidaje da yawa, gwamnatin jiha ta ƙara da katan 23,000 na taliyar yara, buhunan shinkafa 5,000, dawa 500 da buhunan masara 5,000.
Yadda talakawan Jigawa za su amfana
Kwamishinan ayyuka na musamman Hon. Auwal Dalladi Sankara, ya ce an zabo wadanda za su ci gajiyar wannan tallafi daga kananan hukumomi 27 na jihar.
Ya ce rabon kayan abinci ci gaba ne da wasu tsare-tsare na tallafi da Gwamna Umar Namadi ya aiwatar wanda sama da mutane miliyan uku suka amfana.
Wani matashi ɗan Jigawa, Aminu Majeh ya bayyana cewa a kwanakin baya gwamnati ta raba tallafi kuma abin farin cikin ko baka san kowa ba za ka samu.
Aminu ya shaidawa Legit Hausa cewa yana fatan wannan karon ma ka da a sanya siyasa a rabon saboda kowa ya san matsanancin halin kuncin da ake ciki.
"A zahirin gaskiya gwamnatin Ɗanmodi tana kamantawa wajen raba kayan tallafi irin wannan, duk da ban samu ba amma maƙocin mu ya samu, mabuƙata da dama sun samu.
"Ina fatan wannan karon ma ba za a maida abin siyasa ba, domin da zaran an sa siyasa to komai ya lalace. Wallahi mutane na cikin yunwa da wahala Allah ya yaye mana," in ji shi.
Gwamnan Kano ya naɗa kwamishinan tsaro
A wani rahoton kuma Gwamna Abba Kabir ya naɗa Manjo Janar Muhammad Inuwa Idris mai ritaya a matsayin sabon kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida
Abba Kabir ya sanar da wannan naɗin ne a wurin rantsar da majalisun gudanarwa da jami'o'i da manyan makarantu na jihar Kano.
Asali: Legit.ng