'Yan Bindiga Sun Sace Kwamishina da Matarsa a Hanyar Zuwa Ɗaura Auren Ɗiyar Gwamna
- Ƴan bindiga sun yi garkuwa da kwamishinan matasa na jihar Anambra, Agha Mba tare da matarsa a hanyarsu ta zuwa Abuja
- Rahotanni sun nuna cewa kwamishinan ya shiga hannun masu garkuwa ne a hanyar zuwa ɗaurin auren ɗiyar Gwamna Charles Soludo
- Sakataren yaɗa labaran gwamnan Anambra ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce gwamnati ta umarci jami'an tsaro su fara bincike nan take
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Anambra - Rahotannin da ke shigowa sun nuna cewa ‘yan bindiga sun yi garkuwa da kwamishinan matasa na jihar Anambra, Agha MBA, tare da matarsa.
An tattaro cewa an kashe daya daga cikin hadimansa dan garin Onitsha a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa daurin auren diyar Gwamna Charles Chukwuma Soludo.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, 16 ga watan Agusta, 2024 yayin da yake hanyar zuwa babban birnin tarayya Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayanai sun nuna maharan sun sace kwamishinan da mai ɗakinsa a yankin jihar Kogi, suna hanyar zuwa ɗaura auren ɗiyar Gwamna Soludo, wanda za a yi ranar Asabar.
Gwamnatin Anambra ta tabbatar da lamarin
Sakataren yaɗa labaran gwamnan jihar Anambra, Christian Aburime, ya tabbatar da faruwar lamarin inji rahoton Channels tv.
Ya ce har yanzu gwamnati ba ta gano ainihin wurin da aka sace kwamishinan ba amma dai an ambaci wurare biyu, Ubiaja a jihar Edo da kuma jihar Kogi.
Gwamna Soludo ya fara ɗaukar mataki
Ya ce Gwamna Soludo ya fara tuntubar jami’an tsaro don ganin an ceto kwamishinan da matarsa cikin ƙoshin lafiya kuma ba tare da jan lokaci ba.
Aburime ya ce:
“Tuni Oga (Gwamna Soludo) ya fara tuntubar jami’an tsaro don tabbatar da an ceto Kwamishinan da matarsa cikin ƙoshin lafiya kuma ba tare da ɓata lokaci ba."
Yan bindiga sun tashi bom a Anambra
Kun ji cewa ƴan bindiga sun kai mummunan hari kan ƴan sanda a shingen binciken ababen hawa a jihar Anambra da ke Kudu maso Gabas.
Rundunar ƴan sanda ta ce maharan sun yi amfani da bom suka kashe ɗan sanda ɗaya a harin tare da jikkata wani mutum ɗaya.
Asali: Legit.ng