Gwamna Ya Shiga Matsala kan Zargin Rusau ba Bisa Ƙa'ida ba, An Nemi Ya Biya N11bn

Gwamna Ya Shiga Matsala kan Zargin Rusau ba Bisa Ƙa'ida ba, An Nemi Ya Biya N11bn

  • Wata shugabar makaranta Paulin Eboagwu da mai gidanta sun kai ƙarar gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu kan rusa wani sashen filinsu
  • Masu karar sun roki babbar kotun jihar Legas ta umarci waɗanda ake tuhuma su biya diyyar N11bn kan rusa ɓangaren makarantarsu ba bisa ƙa'ida ba
  • Paulin Eboagwu da Daniel Eboagwu sun bayyana cewa sai da suka samu izinin gwamnatin kafin fara aikin gini a filin da ake rigima a kansa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos - Wata shugabar makaranta, Paulin Eboagwu, da mai gidanta, Daniel Eboagwu sun maka Gwamna Babjide Sanwo-Olu a gaban babbar kotun jihar Legas.

Ma'auratan sun shigar da ƙarar gwamnan Legas da wasu mutum shida, suna neman diyyar N11bn kan rusa wani sashin makarantarsu a Ilasan Lekki da ke jihar.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe hadimin gwamna da matarsa, 'yan sanda sun magantu

Babajide Sanwo-Olu.
Masu makaranta sun nemi diyyar N11bn kan rusa wani sashen makarantarsu Hoto: Babajide Sanwo-Olu
Asali: Twitter

Kamar yadda Punch ta tattaro, masu ƙarar ta hannun lauyansu, Babatunde Ademoyo sun yi ikirarin cewa sun bi ƙa'ida kuma da amincewar gwamnan suka gina makarantar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran waɗanda ake tuhuma a karar mai lamba LD/15612LMW/2024 sun haɗa da Antoni Janar na jiha, babban manajan hukumar tsara gine-gine ta Legas, kamfanoni da sauransu.

Yadda zaman shari'ar ta gudana

A zaman kotun ranar Alhamis, masu karar sun shaidawa alƙali cewa sun sayi filin makarantar daga hannun kamfanin Elegushi Property and Investment.

Amma a cewarsu, kamfanin ya dawo ya yi yunƙurin kwace masu wani bangare na filin saboda ya zama cikin wani filin na daban da suka saya.

Sun ƙara da cewa duk da sun gabatar da duk wasu shaidu da takardar amincewar aiki, waɗanda ake ƙara da jami'an gwamnatin Legas sun yi amafani da ƴan daba suka rusa wurin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace kwamishina da matarsa a hanyar zuwa ɗaura auren ɗiyar gwamna

Paulin da Daniele sun nemi kotu ta tabbatar masu da haƙƙinsu na mallakar filin da ya kai mita 1,580.565.

Masu makaranta sun nemi diyyar N11bn

Sannan sun buƙaci kotun ta ayyana matakin shiga filin da ƙarfi da yaji da rusa kadarorin da waɗanda ake tuhuma suka yi a matsayin wanda ya saɓawa doka.

Masu karar sun roƙi kotu ta sa waɗanda ake tuhuma su biya diyyar N1bn na raɗadi da tashin hankali da N10bn na rusa masu kadara ba bisa ƙa"ida ba.

Gidan mai ya kama da wuta a Legas

A wani rahoton kuma Masu sayen man fetur a jihar Legas sun shiga fargaba bayan wuta ta tashi a wani gidan mai ana tsaka da hada-hada.

Wutar ta kama a gidan man mobil da ke kusa da Airport Hotel a titin Obafemi Awolowo a Ikeja, babban birnin Legas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262