NEMA: Mutanen Kano Kusan Miliyan 4 Na Fuskantar Babban Haɗari, Bayanai Sun Fito

NEMA: Mutanen Kano Kusan Miliyan 4 Na Fuskantar Babban Haɗari, Bayanai Sun Fito

  • Hukumar ba da agajin gaggawa ta bayyana cewa kananan hukumomi 14 a jihar Kano na fuskantar barazanar ambaliyar ruwa
  • Shugabar NEMA ta kasa, Zubaida Umar ta ce Kanawa 3,749,200 na cikin haɗari a garuruwa 362 da ke faɗin jihar Kano idan ba a ɗauki mataki ba
  • Rahotanni sun bayyana cewa a makon da ya shige an samu ruwan sama mai yawa a jihar Kano wada ya taƙaita harkokin jama'a na yau da kullum

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA, ta ce ambaliyar ruwa ta taɓa mutane 227, 494 a jihohi 27 na kasar nan.

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da shugaban sashin yaɗa labarai na hukumar NEMA ta kasa, Manzo Ezekiel, ya fitar.

Kara karanta wannan

An shiga fargaba a Kano, NEMA ta lissafa garuruwan da ke fuskantar hadarin ambaliya

Taswirar jihar Kano.
NEMA ta yi hasashen mutane sama da miliyan 3 na fuskantar haɗarin ambaliya a jihar Kano Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Ya ce ambaliyar da ta faru a jihohi 27 ta taɓa mutane da dama ta hanyar rusa gidaje 32,837, lalata gonaki kimanin kadada 16,488 da amfanin gona, Daily Trust ta kawo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NEMA ta yi hasashen ambaliya a Kano

NEMA ta yi gargadin cewa sama da mutane miliyan uku a garuruwa akalla 362 a fadin kananan hukumomi 14 na jihar Kano na fuskantar haɗarin ambaliya.

Rahotanni sun nuna cewa an samu albarkar ruwan sama mai karfi a cikin mako guda da ya gabata a Kano, wanda ya takaita harkokin jama'a a jihar.

Darakta Janar ta hukumar NEMA ta ƙasa, Zubaida Umar ce ta faɗi haɗarin da al'ummar Kano ke ciki a wurin taron ƙarawa juna sani kan shirin magance ambaliya da tsaftace mahalli.

Kodinetan NEMA na Kano, Dr Nuraddeen Abdullahi ya ce hukumar kula da harkokin ruwa ta Najeriya (NIHSA) ta yi hasashen mutane miliyan 3,749,200 na fuskantar hadarin ambaliya.

Kara karanta wannan

Gwamna ya karya farashin buhun shinkafa zuwa N40,000 a Arewa, bayanai sun fito

NEMA ta jero kananan hukumomi 14

Dr. Nuraddeen wanda ya wakilci shugabar NEMA ta kasa, ya ce hasashe ya nuna za a iya samun ambaliya da garuruwa da dama a kananan hukumomi 14 na Kano.

Kananan hukumomin da abin ya shafa sun hada da Rimin Gado, Tofa, Kabo, Madobi, Garun Malam, Bebeji, Rano, Dawakin Kudu, Warawa, Wudil, Sumaila, Ajingi, Kura da Dala.

Tsoffin hadiman Ganduje sun haɗa kai

A wani rahoton kuma jiga-jigan APC da suka riƙe mukaman siyasa a gwamnatin Ganduje sun kafa sabuwar kungiya da manufa guda a jihar Kano.

Shugaban ƙungiyar kuma tsohon manajan darakta na hukumar ruwa ta Kano ya ce tuni suka fara raba tallafin buhunan shinkafa ga mabukata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262