Gwamna Ya Karya Farashin Buhun Shinkafa zuwa N40,000 a Arewa, Bayanai Sun Fito

Gwamna Ya Karya Farashin Buhun Shinkafa zuwa N40,000 a Arewa, Bayanai Sun Fito

  • Gwamna Ahmed Aliyu ya sanar da ragewa al'ummar Sakkwato farashin buhun shinkafa mai girman kilo 50 domin rage masu raɗaɗi
  • Al'ummar jihar Sakkwato za su sayi shinkafa daga hannun gwamnatin Aliyu a farashi mai rahusa, tsakanin N40,000 zuwa N45,000
  • Kwamishinan ƙananan hukumomi na jihar, Ibrahim Adare ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa mai ɗauke da cikakken bayani

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Sokoto - Gwamnatin jihar Sakkwato ƙarƙashin jagorancin Gwamna Ahmed Aliyu ta ƙara azama a ƙoƙarinta na karya farashin kayayyakin abinci na yau da kullum.

Gwamnatin ta fara shirin sayo tirelolin shinkafa 300 tare da sayarwa mutanen Sakkwato a farashi mai rahusa.

Gwamna Ahmed Aliyu.
Gwamna Aliyu ya karya farashin buhun Shinkafa a jihar Sakkwato Hoto: Ahmed Aliyu
Asali: Facebook

Gwamnan Sokoto zai karya shinkafa

Kara karanta wannan

Manyan ƴan siyasa, tsofaffin hadiman Ganduje sun kafa kungiya da manufa 1 a Kano

Kwamishinan kananan hukumomi, Ibrahim Adare ne ya bayyana hakan jim kaɗan bayan kammala taron majalisar zartaswa ta jihar ranar Laraba, 14 ga watan Agusta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce gwamnatin Ahmed Aliyu ta damu matuƙa da halin kuncin da al'ummar kasar nan ke ciki ciki har da mazaunan jihar Sokoto, Punch ta ruwaito.

Buhun shinkafa zai dawo N40,000 Sokoto

Ibrahim ya ce gwamnatin jihar ta amince da sayen tireloli 300 na shinkafa wanda za a sayarwa mazauna jihar a kan rangwame kusan kashi 45% daga farashin kasuwa.

“A ƙoƙarin sauƙaƙa wa al'umma gwamnatin jihar Sakkwato karkashin jagorancin Dakta Ahmed Aliyu, ta yanke shawarar sayo tireloli 300 na shinkafa."
"Za a tura shinkafar zuwa kowace gunduma, kamar yadda muka sani muna da gundumomi 244 a Sakkwato, kowace gunduma za a tura mata tirela daya, kuma za a sayarwa mutane a farashi mai rahusa.

Kara karanta wannan

Katsina: Gwamna ya sauya dokar da ya sanya lokacin zanga zanga a Najeriya

"Gwamnati za ta biya tallafin kusan kashi 55 cikin ɗari. Idan farashin buhun shinkafa N86,000 ne a kasuwa, za mu samar da ita a tsakanin N40,000 zuwa N45,000.”

- Ibrahim Idare.

Kwamishinan ya ƙara da bayanin cewa tallafin na kowa da kowa ne, babu batun banbancin kabila ko jam'iyyar siyasa.

Sarkin Bauchi ya janye sarautar sanata

A wani rahoton kuma Mai Martaba Sarkin Bauchi, Dr. Rilwanu Suleiman Adamu ya sauke Sanata Shehu Buba Umar daga sarautar Majidaɗin Bauchi.

Majalisar masarautar ta ce an ɗauki wannan matakin ne bisa zargin Sanatan da rashin mutunta Gwamna Bala Mohammed.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262