Shekarau Ya Bayyana Wani Babban Sirrinsa Kafin Ya Zama Gwamnan Kano
- Malam Ibrahim Shekarau ya yi magana kan abin da ya mallaka kafin ya fito takarar gwamnan jihar Kano a zaben 2003
- Lokacin da ya yi takara ba shi da N100,000 a cikin asusunsa sannan har ya kusa gama wa'adinsa na biyu bai mallaki gida ba
- Shekarau wanda ya yi gwamna har sau biyu ya ce bai taɓa karɓar wani abu daga hannun ƴan kwangila ba har ya gama mulki
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya bayyana cewa yana da ƙasa da N100,000 a asusunsa lokacin da ya tsaya takarar gwamna.
Ibrahim Shekarau wanda kuma ya taɓa riƙe muƙamin tsohon ministan ilimi, ya jaddada cewa bai taɓa yin katsalandan kan kuɗaɗen ƙananan hukumomi ba a lokacin mulkinsa.
Jaridar The Nation ta ce Shekarau ya bayyana hakan ne yayin taron manema labarai gabanin bikin cikar ƙungiyar ɗalibai musulmi ta Najeriya (MSSN) shekaru 70 da za a fara a ranar 12 ga watan Oktoba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Malam Shekarau wanda shi ne shugaban kwamitin shirya taron, ya yabawa ƙungiyar kan yadda ta taka muhimmiyar rawa a rayuwarsa.
Abin da Shekarau ya mallaka kafin takara
"A lokacin da na tsaya takara, ina da ƙasa da N100,000 a asusuna, kuma shiga ta siyasa ba zaɓin kaina ba ne, sanya ni aka yi."
"Ɓan taɓa amsar wani kaso daga hannun ɗan kwangila ba. Idan akwai wani ɗan kwangila da ya yi aiki da ni a cikin shekarun da suka wuce wanda ya san cewa ya ba ni wani kaso ko ya kawo kuɗi, ya fito ya faɗa."
"Haka kuma babu wani daga cikin kwamishinoni na da ya taɓa kawo min ko Naira ɗaya da sunan wani kaso daga hannun ɗan kwangila."
"Babu shugaban ƙaramar hukumar da ya taɓa ba ni ko Naira ɗaya a shekara takwas da na yi ina mulki. Ɓan taɓa kwasar wani abu daga cikin kuɗaɗensu ba."
"Har zuwa ƙarshen wa'adina na biyu a shekarar 2007, ba ni da gida na ƙashin kai na."
- Malam Ibrahim Shekaru
Matsayar Shekarau kan rikicin sarautar Kano
A wani labarin kuma, tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya yi magana kan rikicin masarautar Kano da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa
Shekarau ya bayyana cewa rikicin na masarautar Kano tsakanin Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero ya dame shi, amma ba ya son tsoma bakinsa a ciki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng