Katsina: Gwamna Ya Sauya Dokar da Ya Sanya Lokacin Zanga Zanga a Najeriya
- Muƙaddashin gwamnan Katsina, Farouk Lawal Jobe ya cire dokar hana fita da aka sanya a ƙananan hukumomin jihar
- Sakataren gwamnatin Katsina, Abdullahi Faskari ne ya bayyana hakan ranar Talata, ya ce mutane na da damar ci gaba da harkokinsu
- Katsina dai na ɗaya daga cikin jihohin da aka samu tashe-tashen hankula a lokacin zanga-zangar adawa da manufofin gwamnati
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Katsina - Gwamnatin jihar Katsina da ke Arewa maso Yammacin Najeriya ta janye dokar hana fita da ta sanya sakamakon rikice-rikicen da suka faru a wasu sassa.
Sakataren gwamnatin jihar, Abdullahi Faskari ne ya bayyana hakan a wata sanarwa ranar Talata, 13 ga watan Agusta, 2024.
Idan ba ku manta ba mukaɗdashin gwamnan jihar Katsina, Farouk Jobe ya sa dokar hana fita saboda tashin-tashinar da aka yi lokacin zanga-zanga, Channels tv ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Masu zanga-zanga sun yi ɓarna
Katsina dai na daya daga cikin jihohin da aka yi tashe-tashen hankula a lokacin zanga-zanga kan tsadar rayuwa wadda masu shiryawa suka ce ta lumana ce.
A rahoton The Nation, masu zanga-zangar sun yi kira ga gwamnatin tarayya karkashin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta sauya tunani kan wasu manufofi kamar cire tallafin mai.
Sai dai tun a ranar farko, zanga-zangar da rikiɗa ta koma tashin hankali yayin da ƴan daba da ake zargin sun shiga cikin masu zanga-zangar suka riƙa aikata laifuka.
Masu zanga-zangar dai sun riƙa bankawa wurare wuta tare da sace-sacen dukiyar al'umma da barnata kayan gwamnati, lamarin da ya sa mahukunta suka ɗauki mataki.
Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta sanar da kama mutane 64 da ake zargi da wawure dukiyar jama’a da barna a lokacin zanga-zangar da aka yi a fadin kasar.
Gwamnatin Katsina ta janye doka
Da yake sanar da cire dokar hana fita, sakataren gwamnatin Katsina ya ce an ɗauki wannan matakin ne domin bai wa jama'a damar ci gaba da harkokinsu.
Wani matashi da ya so fita zanga-zanga a Katsina amma ya fasa saboda abin da ya faru, Mubarak Lawal ya shaida mana cewa matasa sun ɓata rawarsu da tsalle.
Da yake zantawa da wakilin Legit Hausa, matashin ya ce wannan ba ita ce hanyar da ya kamata ƴan Najeriya musamman ƴan uwansa matasa su nuna fushinsu ba.
"Abubuwan da suka faru ba wai a nan Katsina kaɗai ba a dukkan jihohi sun nuna ba zanga-zangar neman ƴanci muka yi ba, ɓarna da sace-sace kawai aka yi.
"Na so shiga wannan zanga-zanga amma tunda na fahimci ba za a kare lafiya ba na janye kaina, ba zai yiwu na shiga na jawo ma kaina wata matsala ba," in ji shi.
An cire dokar hana fita a Jigawa
A wani labarin gwamnatin jihar Jigawa ƙarƙashin jagorancin Gwamna Umar Namadi, ta cire dokar hana fita da ta sanya a ƙananan hukumomi takwas na jihar.
Dokar hana fitan da aka sanya sakamakon rikicin da aka samu a lokacin zanga-zangar nuna adawa da halin ƙunci, yanzu an cire ta gaba ɗaya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng