Jerin Muhimman Abubuwa 3 da Tinubu Ya Kara Masu Kudi Daga Hawa Mulki Zuwa Yau
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
A ranar Asabar, 10 ga watan Agusta, 2024 ne ƴan Najeriya suka gama zanga-zanga ta tsawon kwanaki 10 kan halin da suka tsinci kansu a ciki na tsadar rayuwa.
Masu zanga-zangar sun yi mata take da #EndBadGovernance kuma manyan bukatun da suka nema su ne dawo da tallafin man fetur da sauko da farashin kayayyaki.
Sun koka da cewa tsare-tsaren tattalin arziki da gwamnatin tarayya ta ɓullo da su, sun jefa mafi akarin ƴan ƙasar cikin mawuyacin hali da fatara.
A wannan rahoton, Legit Hausa ta tattaro muku wasu abubuwa da gwamnatin tarayya ta ƙarawa kuɗi bayan rantsar da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinibu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Man fetur
Tun a jawabinsa na wurin rantsuwar kama aiki, shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya sanar da cewa, "tallafin mai ya tafi," ma'ana gwamnati ba za ta sake biyan ko ƙwandala ba.
Jim kaɗan bayan haka ne gidajen mai suka fara rufewa yayin da wasu kuma suka ƙara farashin litar fetur daga kusan N200 zuwa abin da ya haura N500.
Wannan mataki da Shugaba Tinubu ya ɗauka ya jefa da ƴan ƙasar cikin wani hali kuma tun daga wannan lokaci farashin kayayyakin amafanin yau da kullum suka fara hauhawa.
2. Kuɗin ruwa
Gwamnatin tarayya karkashin Bola Ahmed Tinubu ta hannun babban bankin ƙasa CBN ta ƙara kuɗin ruwa aƙalla sau huɗu daga watan Mayu, 2023 zuwa yau.
A watan Yuli, 2023, CBN ƙarƙashin muƙaddashin gwamna, Folashodun Shonubi ya fara ƙara kuɗin ruwa bayan kama aikin zaɓaɓɓen shugaban ƙasa daga 18.50% zuw 18.75%.
Haka nan a watan Fabrairu, 2024 bayan naɗa sabon gwamnan CBN, Olayemi Cardoso ya ƙara ƙuɗin ruwa daga 18.75 zuwa 22.75%.
A watan Maris, CBN ya sake ƙara kuɗin ruwa zuwa 24.75% daga 22.75%, sannan ya kuma ɗaga shi daga 24.75% zuwa 26.25% a watan Mayu, in ji The Cable.
Mako uku da suka wuce, CBN a taron kwamitin MPC karo na 296 ya sake ƙara kuɗin ruwa zuwa 26.75 duk da hauhawar farashin kayayyakin da ake fama da shi.
Kamar yadda Channels tv ta ruwaito, gwamnan CBN ya ce sun ɗauki wannan mataki ne da zummar daƙile hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya.
3. Harajin shigo da kaya daga ƙetare
Gwamnatin tarayya ta hannun hukumar kwastam ta kasa ta kara farashin kuɗin harajin da ake biya yayin shigo da kayayyaki daga kasashen ketare zuwa Najeriya.
Hakan ya biyo bayan tashin farashin canjin Dala wanda hukumar kwastam mai kula da harkokin safara a Najeriya ke amfani da shi wajen kayyade harajin.
A watan Disamban 2023, hukumar kwastam ta ɗaga farashin kudin safarar kayayyaki daga N783 kan kowace Ɗalar Amurka zuwa N952.
Ta ɗauki wannan matakin ne a lokacin da farashin canjin Dala ya tashi zuwa kusan N1000/$ a kasuwar hada-hadar kudi.
To sai dai a baya-bayan nan farashin canjin ya ƙara tashi daga 1,600/1$ zuwa 1,618.732, lamarin da masu safarar kayayyaki ta ruwa da ta sama suka koka kan tsadar haraji.
Wasu ƴan kasuwa sun ce a yanzu harajin kwantena mai tsawon ƙafa 40 ya kai N20m maimakon N7m da suka biya a watan Disamba, 2023.
Jerin tallafi 11 na Gwamnatin Tarayya
A wani rahoton kuma ’yan Najeriya na da damar neman akalla tallafi 11 da gwamnatin tarayya ta kirkiro domin saukakawa al'ummar kasar.
Waɗannan manyan shirye shiryen sun shafi fannoni kamar ilimi, sufuri, kasuwanci, gidaje da sana'o'in dogaro da kai.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng