Gwamnan Ya Bi Hanyar Lalama, Ya Roki Matasa Su Rungumi Zaman Lafiya a Arewa
- Gwamnan jihar Benuwai ya yi kira da roƙo ga matasa su daina shiga ayyukan laifi, su rungumi zaman lafiya domi samun ci gaba
- Hyacinth Alia ya bayyana cewa duk wani ƙoƙari da gwamnati ke yi domin gyara goben matasa ne,ya roki su kama hanya mai ɓullewa
- Gwamna Alia ya yi wannan roko ne a jawabin da ya yi a ranar matasa ta duniya kwanaki kaɗan bayan kammala zanga-zanga
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Benue - Gwamna Hyacinth Alia na jihar Benue ya roki matasa da su rungumi zaman lafiya domin kawo ci gaban da ake bukata a jihar.
Gwamna Alia ya yi wannan roƙo ne a jawabin da ya yi na ranar matasa ta duniya wanda aka watsa kai tsaye yau Talata, 13 ga watan Agusta.
Gwamna Alia ya tura saƙo ga matasa
Ya ƙara da cewa yana sane da matsalolin da mutane ke ciki sakamakon rashin tsaron da ake fama da shi a sassan jihar, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Ina da masaniyar halin da ake ciki sakamakon matsalar tsaro, wanda abin takaicin shi ne har da matasan mu a cikin masu jefa mu cikin ƙunci.
"Ina kira ga wadanda suke da hannu wajen haddasa fitina da su ajiye makamansu, su rungumi zaman lafiya, su taho mu tattauna.
Shaye-shayen kwayoyi, kungiyoyin asiri, damfarar intanet da aka fi sani da Yahoo da sauran munanan dabi’u su ne gurɓatatun halayen da nake rokon matasa su guji faɗawa ciki.
- Gwamna Hyacinth Alia.
Abin da gwamnatin Benuwai ke yi wa matasa
Alia ya ƙara da cewa duk kokarin da suke yi na gina jihar Benuwai domin inganta goben matasa ne, inda ya ƙara roƙon matasa ka da su ruguza wannan ƙoƙari da ake yi, rahoton The Sun.
Gwamnan ya jaddada cewa aikata miyagun laifuka ba shi da wata riba face mutuwa, amma aiki tuƙuru cikin zaman lafiya kuwa na kawo nasara a rayuwa.
Gwamnan ya jaddada cewa matasa sun kai kashi 60% na al’ummar Binuwai, yana mai cewa “Ba ku ne goben mu kawai ba, ku ne ƙarfinmu da tudun da aka gina Benue a kai."
Gwamnatin Neja ta ɗauki matakan kawo sauƙi
A wani rahoton kuma gwamnatin jihar Neja karƙashin jagoranci Muhammed Umaru Bago ta yi alkawarin bullo da shirye-shiryen ragewa mutane radaɗin rayuwa.
Muƙaddashin gwamnan jihar, Kwamared Yakubu Garba ya yabawa masu ruwa da tsaki, ƴan jihar Neja bisa yadda suka tsame kansu daga zanga-zanga.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng