Ministan Tinubu Ya Yi Nasara, Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Masu Zanga Zanga
- Ministan babbar birnin tarayya Abuja ya yi nasara a bukatar da ya shigar gaban kotu kan masu zanga-zangar tsadar rayuwa
- Mai shari'an ya amince da bukatar Nyesom Wike na tsawaita umarnin taƙaita zanga-zanga a filin wasa na ƙasa MKO Abiola
- Wannan na zuwa ne bayan wasu daga cikin jagororin zanga-zangar da aka yi sun yi barazanar ci gaba fiye da kwanaki 10
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Babbar kotun birnin tarayya Abuja ta tsawaita dokar taƙaitawa masu zanga-zanga a filin wasa na MKO Abiola.
Mai shari'a Sylvanus Oriji ne ya yanke hukunci tsawaita wannan umarni a zaman ranar Talata, 13 ga watan Agusta, 2024.
Alkalin ya bayar da umarnin ne biyo bayan bukatar da Dr Ogwu Onoja SAN ya shigar a madadin Ministan Babban Birnin Tarayya, kamar yadda The Nation ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zanga-zanga: Ministan Abuja ya je kotu
A ci gaba da zaman shari'ar yau Talata, babu daya daga cikin wadanda ake tuhuma 12 da ya bayyana a gaban kotu kuma ba su turo lauyoyi ba.
Wadanda ake ƙara su ne Omoyele Sowore, Damilare Adenola, Adama Ukpabi, Tosin Harsogba, sufeto janar na ‘yan sanda, kwamishinan ‘yan sanda da wasu da ba a sani ba.
Sauran sun hada da daraktan hukumar DSS, daraktan hukumar NSCDC, Babban Hafsan Sojin Kasa, Babban Hafsan Sojin Sama, Babban Hafsan Sojin Ruwa a matsayin waɗanda ake ƙara na 1 zuwa 12.
Wike ya miƙa bukata ga kotu?
Ministan Abuja ta bakin lauyansa, ya ja hankalin kotu kan wata sanarwa da Damilare Adenola ya fitar cewa za a iya tsawaita zanga-zangar ta wuce kwanaki 10 na farko.
Onoja SAN ya shaidawa kotun cewa waɗanda ake ƙarar ba su zo zaman kotu ba don haka babu wanda ya san abin da suke ƙullawa na gaba, Channels tv ta tattaro.
Wane hukunci kotu ta yanke?
A wani takaitaccen hukunci da alkalin ya yanke, ya amince da bukatar kuma ya tabbatar da cewa umarnin taƙaita zanga-zangar na ranar 31 ga watan Yuli yana nan daram.
Mai shari’a Oriji ya amince ƴan Najeriya na da ƴancin gudanar da zanga-zanga, amma ya takaita su a filin wasan saboda fargabar abin da ka iya zuwa ya komo.
Gwamna ya cire doka a Kaduna
A wani labarin kuma Uba Sani ya janye dokar hana fita gaba ɗaya a cikin garin Kaduna da Zaria bayan abubuwan da suka afku lokacin zanga zanga.
Kwamishinan tsaron cikin gida ya ce daga yanzu jama'a na da damar gudanar da harkokinsu na halak ba tare da wata tsangwama ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng