Jirgi Ɗauke da Mutane Sama da 20 Ya Gamu da Haɗari a Arewa, An Rasa Rayuka

Jirgi Ɗauke da Mutane Sama da 20 Ya Gamu da Haɗari a Arewa, An Rasa Rayuka

  • Wani Kwale-kwale ɗauke da mutane 24 ya gamu da haɗari a kauyen Dundaye da ke karamar hukumar Wamakko a Sakkwato ranar Lahadi
  • Hukumar ba da agajin gaggawa NEMA ta ce zuwa yanzu jami'ai da taimakon mutanen yankin sun ciro gawar mutum huɗu
  • Ta kuma bayyana cewa an ceto mutum 19 da ransu yayin da ya rage sauran mutum ɗaya, ana ci gaba da lalube a ruwan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Sokoto - Akalla mutane hudu ne suka mutu a wani hatsarin jirgin ruwa da ya auku a kauyen Dundaye da ke karamar hukumar Wamakko a Sakkwato.

Shugaban sashen ayyuka na na hukumar bada agajin gaggawa ta kasa (NEMA) reshen jihar Sakkwato, Alhaji Aliyu Kafindangi ya tabbatar da faruwar lamarin.

Kara karanta wannan

Gwamna ya janye dokar hana Fita a Kaduna da Zaria, Ya Aikawa Malamai, Sarakuna Saƙo

Taswirar jihar Sokoto.
Mutane hudu sun mutu a hatsarin jirgin ruwa a jihar Sakkwato Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Sokoto: Jami'ai sun ciro gawar mutum 4

Ya ce haɗarin Kwale-kwalen ya auku ne da yammacin ranar Lahadi da ta gabata, kamar yadda jaridar Punch ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alhaji Aliyu ya ce tawagar jami'an hukumar NEMA, Red Cross ta Najeriya, hukumar kwana-kwana da hukumar agaji Sakkwato ne suka tsamo gawar muttum huɗu.

A cewarsa, jami'an tare da haɗin guiwa mutanen yankin waɗanda suka kware a shiga ruwa ne suka ciro gawarwakin ranar Litinin, rahoton Vanguard.

Yadda haɗarin jirgin ya auku a Sokoto

Aliyu Kafindangi ya ce:

"Daga bayanan da muka samu, mun gano cewa haɗarin ya rutsa da mutum 24 ne kuma kawo yanzun an yi nasarar ceto mutum 19 da ransu. Ranar Lahadi da yamma an ciro gawa ɗaya.
"Sannan jiya Litinin a kara ciro gawarwakin mutum uku, jimulla mutum huɗu kenan suka mutu. Sauran mutun ɗaya ne ba a gani ba amma ana ci gaba da lalube.

Kara karanta wannan

An shiga jimami a Arewacin Najeriya, mata da miji da 'ya'yansu 5 sun mutu bayan cin rogo

Jami'in NEMA ya kuma ƙara da godewa gwamnatin jihar Sakkwato da ƙaramar hukumar Wamakko da sauran al'umma bisa taimakon da suka bayar a aikin ceton waɗanda haɗarin ya rutsa da su.

Jirgin ruwa ya nutse a Jigawa

Rahotanni sun yi nuni da cewa an samu kifewar kwale kwale da wasu yan kasuwa a jihar Jigawa da ke Arewa maso yammacin Najeriya.

Rundunar yan sandan jihar Jigawa ta tabbatar da faruwar lamarin ta kuma yi bayani kan irin asarar da aka tafka yayin hadarin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262