Mutane Sun Kara Samun Sauƙi Bayan Tashin Tashinar Masu Zanga Zanga a Arewa

Mutane Sun Kara Samun Sauƙi Bayan Tashin Tashinar Masu Zanga Zanga a Arewa

  • Gwamna Caleb Mutfwang na Filato ya ƙara sassauta dokar hana zirga-zirga a Jos, babban birnin jihar daga ranar Talata
  • Daga yanzun mazauna Jos na da ikon fitowa su yi harkokinsu na yau da kullum daga karfe 7:00 na safe zuwa 7:00 na yammaci
  • Wannan na zuwa ne bayan sanya dokar kulle sakamakon tashin hankalin da ya biyo bayan zanga-zangar kuncin rayuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Plateau - Gwamnatin jihar Filato ƙarƙashin jagorancin Gwamna Caleb Mutfwanga ta sake sassauta dokar hana fita da ta kaƙaba a birnin Jos-Bukuru.

Gwamnatin ta sanya dojar hana zirga-zirga ta tsawon sa'o'i 24 a babban birnin Jos ne sakamakon tashin-tashinar masu zanga zanga a yankin.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Matasa sun aiki gwamna da sako zuwa ga Tinubu, sun zayyana bukatunsu

Gwamna Mutfwang.
Zanga-zanga: Gwamnatin Plateau ta ƙar sassauta dokar hana fita Hoto: Caleb Mutfwang
Asali: Facebook

Mai magana da yawun gwamnan Filato, Mista Gyang Bere ne ya bayyana kara sassauta dokar a wata sanarwa ranar Litinin a Jos, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Muftwan ya rage dokar kulle

Mista Bere ya ce Gwamna Mutfwang, wanda ya ba da umarnin kara sassauta dokar hana fita, ya ce a yanzu mutane na da damar fita tsakanin karfe 7:00 na safe zuwa 7:00 na yamma.

A cewarsa wannan matakin zai fara ne daga gobe Talata, 13 ga watan Agusta, 2024, yana mai cewa dokar kullen za ta rika aiki daga 7:00 na dare zuwa 7:00 na safe, Daily Post ta kawo.

A ranar Lahadi, 4 ga watan Agusta ne gwamnatin Filato ta kafa dokar hana fita, biyo bayan wawure dukiyar gwamnati da ta jama'a da sunan zanga zanga a karamar hukumar Jos ta Arewa.

Kara karanta wannan

Ana shirin gama zanga zanga, gwamna ya sake daukar sabon mataki

Dalilin sassauta dokar kulle a Jos

Bere ya ce matakin na kara sassauta dokar hana fita ya biyo bayan shawarwarin da hukumomin tsaro suka bayar kan halin da ake ciki yanzu na dawowar kwanciyar hankali.

"Duba da yadda aka samu ci gaba a yanayin tsaro a birnin Jos-Bukuru, gwamnatin Filato ta kara sassauta dokar hana fita daga ranar Talata 13 ga watan Agusta.
“Yanzu jama'a na da damar fita su gudanar harkokinsu na yau da kullum a tsakanin 7:00 na safe zuwa 7:00 na yamma kullum," in ji shi.

Rikicin siyasa ya kaure a Edo

A wani rahoton rigima ta ƙara ɓallewa tsakanin gwamnatin Edo da Kwamared Philip Shaibu, mataimakin gwamnan da kotu ta mayar.

Shaibu ya sanar da cewa ya koma bakin aiki ranar Litinin amma Gwamna Obaseki ya maida martani da cewa sojan gona ne.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262