'Yan Sanda Sun Saɓawa da Gwamna a Arewa Kan Wutar da Ta Kama a Wurin Ibada

'Yan Sanda Sun Saɓawa da Gwamna a Arewa Kan Wutar da Ta Kama a Wurin Ibada

  • Rundunar ƴan sanda reshen jihar Neja ta saɓawa Gwamna Muhammed Umar Bago kan musabbabin tashin gobara a wata cocin Kontagora
  • A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamna ta fitar, ta ce wasu ƴan daba ne suka bankawa cocin wuta amma ƴan sanda sun ce ba su gano komai ba
  • Kakakin ƴan sandan jihar Neja, Wasiu Abiodun ya bayyana cewa suna kan bincike kan lamarin kuma ba su gano abin da ya jawo gobarar ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Niger - Rundunar ‘yan sanda ta saɓawa gwamnatin jihar Neja kan musabbabin tashin gobara a hedikwatar cocin Redeemed Christian Church of God da ke Kontagora.

Gwamnatin Neja karkashin jagorancin Gwamna Umaru Bago ta zargi ƴan daba da banka wuta a cocin amma rundunar ƴan sanda ta ce ba haka ba ne.

Kara karanta wannan

Ana shirin gama zanga zanga, gwamna ya sake daukar sabon mataki

Gwamna Umar Bago.
Yan sanda sun yi saɓani da gwamnatin Neja kan ƙona coci a Kontagora Hoto: Umar Bago
Asali: Twitter

Kamar yadda Daily Trust ta rahoto, rundunar ƴan sanda reshen jihar Neja ta ce har kawo yanzu ba a gani asalin dalilin barƙewar gobara a qurin ibadar kiristan ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Bago ya ɗora laifin kan ƴan daba

Gwamnatin jihar Neja a wata sanarwa da mai baiwa gwamna shawara ta kan harkokin yada labarai, Aisha Wakaso ta fitar, ta ce wasu ‘yan daba ne suka kona cocin.

Umar Bago ya bayyana harin a matsayin wnai yunƙuri na kawo cikas ga zaman lafiya da hadin kai a jihar, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Amma a wata sanarwa da ya fitar kan lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Neja, SP Wasiu Abiodun ya ce ba ‘yan daba ne suka kona cocin ba.

Me ya haddasa tashin gobara?

"A ranar 10.ga watan Agusta, 2024 mun samu rahoton cewa gobara ta tashi a Redeemed Church da ke titin COE a Kontagora da misalin ƙarfe 4:00 na asubahi.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai harin 'bom' kan jami'an tsaro, an yi asarar rai a Najeriya

"Gobarar ta kone tare da lalata dukiyoyi masu muhimmanci a cocin, wandanda har yanzu ba a tantance kimarsu ba. 'Yan sanda karkashin jagorancin DPO na ofishin Kontagora sun ziyarci wurin.
“Har yanzu ba a gano musabbabin tashin gobarar ba yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin, babu wanda ya rasa ransa."

Lukman ya soki Tinubu da gwamnoni

A wani rahoton kuma tsohon mataimakin shugaban APC na Arewa maso Yamma, Salihu Lukman, ya yi iƙirarin cewa tsarin dimokuradiyyar Najeriya ba ya aiki.

Lukman ya bayyan acewa halin da ƙasar nan ke ciki kaɗai ya isa a sauke shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da wasu gwamnoni.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262