Gwamna a Arewa Ya Taso Masu Zanga Zanga a Gaba, Ya Yi Kakkausan Kashedi
- Gwamnatin Kaduna ta gargaɗi matasa cewa ba za ta lamunci duk wata zanga zanga ba tare da izinin hukumomin tsaro ba
- Kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan ya ce sun gano wasu miyagu da ke shirin fakewa da zanga zanga su tayar da fitina a Kaduna
- Aruwan ya ce daga yanzu gwamnati ta haramta duk wani gangami da bai samu sahalewar jami'an tsaro ba a faɗin jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kaduna - Gwamnatin jihar Kaduna ta yi gargadin cewa daga yanzu ba za ta lamunci duk wata zanga-zangar da hukumomin tsaro ba su amince da ita ba.
Gwamnatin karkashin Malam Uba Sani ta ce ɓata gari na amfani da irin wannan zanga-zangar wajen wawushe dukiyar gwamnati da ta al'umma, don haka ta taka ma abin burki.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya wallafa a shafinsa na X ranar Asabar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Kaduna ta gindaya sharaɗi
Ya ce gwamnatin Kaduna ba za ta sake lamuntar mummunan lamarin da ya auku a ranar 1 ga watan Agsuta, ranar da aka fara zanga-zanga ya kara faruwa ba.
Aruwan ya ce munanan abubuwan da suka faru a ranakun 1 da 5 ga watan Agusta alamu ne karara da ke nuna miyagu na kulla yadda za su angiza Kaduna cikin tashin hankali.
"Gwamnatin Kaduna da jami'an tsaro ba za su tsaya suna kallo masu manufar ruguza jihar su cimma nasara ba tare da ɗaukar mataki ba.
"Muna ƙara kashedi da babbar murya cewa ba za mu bar duk wasu miyagu da ke fakewa da sunan zanga zanga su tayar mana da tarzoma ba.
- Samuel Aruwan.
Abin da doka ta tanada kan zanga-zanga
Kwamishinan ya ƙara da cewa duk da mutane na da ya halatta mutane su yi zanga-zanga a dokar ƙasa, amma haram ne yin duk wani gangami da tare da sahalewar hukumomin tsaro ba.
Matasa sun fito zanga-zanga a Abuja
Kun ji cewa masu zanga zanga sun sake tururuwa a kan tituna a babban birnin tarayya Abuja yau Asabar, 10 ga watan Agusta, 2024.
Tuni dai ƴan sanda suka ƙara tsaurara tsaro a kwaryar birni tun ranar Jumu'a saboda masu zanga-zanga na shirin rufewa da gagarumin tattaki.
Asali: Legit.ng