Ana Shirin Gama Zanga Zanga, Gwamna Ya Sake Daukar Sabon Mataki

Ana Shirin Gama Zanga Zanga, Gwamna Ya Sake Daukar Sabon Mataki

  • Gwamnatin jihar Plateau ƙarƙashin jagorancin Gwamna Caleb Mutfwang ta sake sassauta dokar hana fita da ta sanya a Jos da Bukuru
  • Gwamnatin a cikin wata sanarwa ta bayyana cewa jama'a za su iya fitowa daga ƙarfe 10:00 na safe zuwa ƙarfe 6:00 na yamma
  • Gwamna Mutfwang ya kuma yabawa jama'a bisa kishin da suka nuna tare da haɗin kan da suka bayar kan sanya dokar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Plateau - Gwamnatin jihar Plateau ta sake sassauta dokar hana fita da ta sanya a Jos-Bukuru.

Hakan ya biyo bayan ingantuwar yanayin tsaro a yankunan da kuma yadda mutane suka bi dokar hana fitan sau da ƙafa.

Gwamnatin Plateau ta sassauta dokar hana fita
Gwamnatin Plateau ta sake sassauta dokar hana fita a Jos da Bukuru Hoto: Caleb Mutfwang
Asali: Facebook

Gwamna Mutfwang ya sassauta dokar hana fita

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Gwamnan Plateau ya dauki matakin saukakawa jama'a

Da yake bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Asabar, daraktan yaɗa labarai da hulda da jama'a na gwamnan jihar, Gyang Bere, ya ce matakin zai fara aiki daga ranar Asabar, 10 ga Agusta, 2024, cewar rahoton tashar Channels tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa a yanzu an ba mazauna yankunan izinin gudanar da ayyukansu tsakanin ƙarfe 10:00 na safe zuwa 6:00 na yamma a kowace rana, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.

"Daga ranar Asabar, 10 ga watan Agusta, 2024, an ba mazauna yankunan izinin gudanar da harkokinsu na yau da kullum daga ƙarfe 10:00 na safe zuwa 6:00 na yamma a kowace rana."
"Mai girma Gwamna Caleb Manasseh Mutfwang ne ya amince da wannan matakin, biyo bayan shawarwarin da hukumomin tsaro suka bayar."
"An sake sassauta dokar ne domin ba jama'a damar ci gaba da gudanar da harkokin neman na abincinsu yayin da ake tabbatar da zaman lafiya."

Kara karanta wannan

Bayan Mangal, wani gwamna a Arewa ya sa hannu a fara aikin gina kamfanin siminti

- Gyang Bere

A cewar sanarwar, gwamna Mutfwang ya miƙa godiyarsa ga jama'a bisa kishin da suka nuna da haɗin kan da suka bayar a wannan lokacin mai wahala.

Matakin ya yi daidai

Legit Hausa ta samu jin ta bakin wani mazaunin birnin Jos mai suna Ziya'ul Dauda Adamu, wanda ya yaba da matakin da gwamnan ya ɗauka na sake sauƙaƙawa jama'a.

Ya bayyana cewa tabbas dokar ta yi amfani wajen hana ɓarƙewar rikici bayan da ƴan daba suka yi kutse a cikin zanga-zangar.

"Eh wannan mataki ne mai kyau domin mutane za su ƙara samun sauƙi wajen gudanar da harkokinsu na yau da kullum. A yanzu hankula sun kwanta sosai."

- Ziya'ul Dauda Adamu

Gwamna Mutfwang ya koka kan tsadar rayuwa

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang ya koka kan yadda kayayyaki suka yi tsada sosai a Najeriya.

Gwamna Caleb Mutfwang ya bayyana cewa mutane suna iƙirarin cewa Bola Tinubu ya ƙara musu kuɗin shiga amma darajar kuɗin ta yi baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng