Zanga zanga: Ƙasar Poland Ta Fara Kamun Ƙafa domin a Saki mutanenta da Aka Kama a Kano
- Ƙasar Poland ta roƙi Najeriya ta haƙura da saki ƴan ƙasarta da aka kama da laifin ɗaga tutocin Rasha lokacin zanga-zanga a Kano
- Mataimakin ministan harkokin wajen ƙasar, Jakub Wisniewski ya ce ƴan Poland bakwai da aka kama sun aikata laifin ne cikin jahilci
- Jami'an DSS dai sun tabbatar da cafke mutum bakwai ƴan asalin kasar Poland da ke nahiyar Turai bisa zargin ɗaga tutar Rasha yayin zanga-zanga
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Gwamnatin kasar Poland ta roki Najeriya ta saki ‘yan ƙasarta bakwai da aka kama a Kano bisa zargin ɗaga tutar Rasha yayin zanga-zangar yunwa da aka yi.
Mataimakin ministan harkokin wajen Poland, Jakub Wisniewski ne ya yi wannan roko yayin ganawa da jami'an diflomasiyyar Najeriya a birnin Warsaw.
Ya roƙi gwamnatin Najeriya karkahin Bola Ahmed Tinubu ta yi hakuri da saƙi ƴan ƙasar Poland bakwai da aka kama, lakcara da ɗalibai shida, The Nation ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Poland ya roki alfarmar Najeriya
Ya ce waɗanda jami'an tsaron Najeriya suka kama sun shigo Najeriya ne daga jami'ar Warsaw domin halartar taron harshen Hausa.
"A taron na yi bayanin cewa na gamsu ɗaliban sun yi kuskure kuma ɗabi'arsu ta nuna sun aikata haka ne saboda rashin sanin al'adu da dokokin cikin gida a Najeriya.
"Ina rokon mahukunta su duba yiwuwar sako su, su dawo Poland zuwa cikin iyalansu domin danginsu sun ƙagu su sake haɗuwa da ƴan uwansu," in ji Wisniewski."
Alaƙar Polanda da Rasha
Amma Wisniewski ya ƙi yarda cewa ɗaliban sun ɗaga tutocin Rasha a fili saboda ba kasafai ake samun masu goyon bayan Rasha ba a ƙasar Poland, rahoton Notes Poland.
Poland da ke tsakiyar Turai ba za ta manta da lokacin da take a ƙarƙashin mulkin Rasha ba kuma 'yan kasar sun yi suka kan abin da suke kallo a matsayin zaluncin Rasha a Ukraine.
Wisniewski ya ƙara da cewa ƴan Poland bakwai da DSS ta kama an maida su Abuja kuma suna cikin koshin lafiya, yana mai rokon gwamnati ta taimaka ta sake su.
Shekarau ya ba Tinubu shawara
Kuna da labarin cewa Malam Ibrahim Shekarau ya buƙaci gwamnatin Bola Tinubu ta sake nazari kan manufofin tattalin arzikin da ta aiwatar tun bayan hawa mulki.
Tsohon gwamnan Kano ya ce lokaci ya yi da Shugaba Tinubu da hadimansa za su waiwayi baya, su amince da kura-kuransu.
Asali: Legit.ng