Masu Garkuwa da Ɗaliban Jami'a a Arewa Sun Turo Saƙo Mai Ɗaga Hankali
- Masu garkuwa da ɗaliban jami'ar jihar Kogi (KSUK) sun turo sakon kuɗin fansar da suke bukatar a biya kafin su sake su
- Maharan sun sace ɗaliban jami'ar su biyu tare da kantoman karamar hukumar Kabba/Bunu da hadimansa ranar Jumu'a, 2 ga watan Agusta
- Iyayen ɗaliban sun roki gwamnatin Kogi ta taimaka ta ceto ƴaƴansu yayin da ƴan sanda suka ce ba su da masaniya kan lamarin
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kogi- Ƴan bindigar da suka yi garkuwa da ɗalibai biyu na jami'ar jihar Kogi da ke Kabba (KSUK) sun aiko da saƙon adadin kuɗin fansar da suke buƙata.
Masu garkuwar sun nemi a lale masu kuɗi N10m gabanin su sako ɗaliban da ke tsare a hannun su.
Yaushe aka sace ɗaliban jami'ar Kogi?
Kamar yadda jaridar Leadership ta tattaro, ƴan bindiga sun sace ɗaliban jami'ar ne a makon jiya ranar Jumu'a, 2 ga watan Agusta, 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Maharan sun sace ɗaliban tare da shugaban riƙo na ƙaramar hukumar Kabba/Bunu, Dare Michael da wasu hadimansa.
Sai dai ƴan bindigar sun sako ciyaman din saboda ba shi da gamsasshiyar lafiyar da zai iya tafiya zuwa cikin jeji yayin da suka tafi da hadimansa da ɗaliban KSUK.
Masu garkuwa sun nemi kuɗin fansa
Da farko a ranar Litinin da ta gabata, masu garkuwan sun buƙaci a lale masu N100m a matsayin kuɗin fansar hadiman ciyaman din da ɗaliban jami'ar.
Amma daga bisani sun rage adadin kuɗin daga N100m zuwa N10m kafin sako mutanen da ke tsare a hannunsu, kamar yadda Channels tv ta rahoto.
Tuni dai iyayen ɗaliban suka roƙi gwamnatin Kogi ta kawo masu ɗauki wajen kuɓutar da ƴaƴansu, suna masu jaddada cewa tun bayan faruwar lamarin suka rasa kwanciyar hankali.
Wane mataki ƴan sanda suka ɗauka?
Rundunar ‘yan sandan jihar Kogi ta ce ba ta da masaniyar cewa daliban makarantar na cikin wadanda aka sace tare da Mista Dare.
Da aka tuntuɓi jami’in hulda da jama’a na rundunar, SP William Aya, ya tambayi dalilin da ya sa har yanzu iyayen daliban ba su kai rahoto ga jami’an tsaro ba.
Yan bindiga sun ɗauki malami a Zaria
A wani rahoton kuma ƴan bindiga sun kutsa kai cikin gida, sun yi awon gaba da babban malamin addinin Musulunci Sheikh Isma'il Gausi a Zaria da ke jihar Kaduna
Wata majiya daga yankin ta bayyana cewa ƴan bindigar sun yi harbe-harbe domin tsorata mutane kafin su tafi da malamin ranar Laraba
Asali: Legit.ng