Kaico: Ƴan Bindiga Sun Hallaka Basarake, Sun Yi Awon Gaba da Mata da Ƙananan Yara

Kaico: Ƴan Bindiga Sun Hallaka Basarake, Sun Yi Awon Gaba da Mata da Ƙananan Yara

  • Ƴan bindiga sun kashe Magajin Gari da wani mutum a lokacin da suka kai hari kauyen Gefe da ke ƙaramar hukumar Kajuru a Kaduna
  • Wani shugaban al'umma, Markus Ɗanja ya ce maharan sun buɗe wuta kan mai uwa da wabi, sannan sun tafi da mata da ƙananan yara
  • Ya ce har yanzun ba su gama tantance adadin mutanen da maharan suka yi garkuwa da su ba, inda ya ƙara da cewa har da iyalan ɗan uwansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna - Ƴan bindiga sun kai hari kauyen Gefe da ke yankin Kufana a karamar hukumar Kajuru a jihar Kaduna, sun kashe dagacin kauyen da wani mutum guda.

Rahotanni sun nuna cewa bayan haka maharan sun yi awon gaba da wasu mutanen kauyen da dama da suka hada da mata da kananan yara. 

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Sojoji cun ci karo da gomman matasa a cikin mota, sun ɗauki mataki

Taswirar jihar Kaduna.
Yan bindiga sun hallaka Magajin Gari, sun tafi da mutanensa a jihar Kaduna Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 12:00 na tsakar daren wayewar garin Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mahara sun kashe basarake a Kaduna

Wani shugaban al’umma kuma dan uwan ​​daya daga cikin wadanda lamarin ya shafa, Markus Danja ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Juma’a.

Ya ce ɓarayin dajin sun harbe mutane biyu har lahira cikin har da Magajin Garin wanda aka bayyana da Mista Emmanuel Idan, rahoton The Sun.

Mista Markus ya ce:

"Ƴan bindigar na zuwa suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi bayan sun kewaye ƙauyen, duka waɗanda ke waje suka ruga suka ɓuya.
"Abin takaici Mai Unguwa na cikin waɗanda harin ya rutsa da su a waje kuma aka harbe shi a lokacin da yake ƙokarin guduwa. Ɗayan kuma har ɗaki suka je suka kashe shi, suka tafi da matarsa."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai mummunan hari, sun kashe mutane sama da '30' a Arewa

Ƴan bindiga sun sace mata da yara

Markus ya ce suna kokarin tattara bayanai da adadin mutanen da aka yi garkuwa da su ko suka ɓata, ya kara da cewa matan dan uwansa da ‘ya’yansa na cikin waɗanda suka ɓata.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, Gwamnatin Kaduna da rundunar ‘yan sandan jihar ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.

Benue: Mahara sun kashe mutum 30

A wani rahoton kun ji cewa ƴan bindiga sun kashe akalla mutane 30 a kauyen Ayati, ƙaramar hukumar Ukum a jihar Benuwai da ke Arewa ta Tsakiya.

Mazauna yankin sun bayyana cewa da yiwuwar waɗanda aka kashe a harin su haura 50 saboda har yanzun ana kan binciken gawarwaki yau Jumu'a.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262