Bayan Mangal, Wani Gwamna a Arewa Ya Sa Hannu a Fara Aikin Gina Kamfanin Siminti

Bayan Mangal, Wani Gwamna a Arewa Ya Sa Hannu a Fara Aikin Gina Kamfanin Siminti

  • Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya rattaba hannu kan yarjejeniyar fara aikin gina masana'antar siminti
  • Bala Mohammed ya rattaɓa hannu kan yarjejeniyar MoU da kamfanin Resident Cement Factory Limited na fara gina masana'antar a farkon 2025
  • Gwamnan ya bayyana cewa kamfanin simintin da za a gina sai samar da ayyukan yi a jihar Bauchi da ƙarin kuɗaɗen shiga

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bauchi - Gwamnan Bauchi Bala Mohammed ya rattaba hannu kan yarjejeniya da Resident Cement Factory Limited domin kafa kamfanin siminti na $1.5bn a jihar.

Bala Mohammed ya sa hannu kan wannan yarjejeniya ranar Laraba, 7 ga watan Agusta, 2024, in da ya ce hakan na cikin yunƙurin gwamnatinsa na sauƙaƙa kasuwanci.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya shiga matsala kan sukar Tinubu, an yi masa tonon silili

Kamfanin siminti.
Gwamna Bala Mohammed ya sa hannu kan yarjejenuyar gina masana'antar siminti a jihar Bauchi Hoto: Bet_noire
Asali: Getty Images

Gwamnan ya ƙara da cewa a halin yanzu masana'antar simintin da ake ginawa ta kai matakin tantancewa gabannin fara aiki, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bauchi: Abubuwan da aikin simintin ya ƙunsa

Ya ce kuɗin da aka ware $1.5bn za a yi amfani su wajen gina dam, tashar manyan motoci, gidaje, da sauran ababen more rayuwa a garin Gwana da ke karamar hukumar Alkaleri.

Gwamna Bala ya ce gwamnatinsa za ta inganta harkokin kasuwanci ta yadda ba za a riƙa samun cikas ba, kuma za ta jawo jama'a a jiki domin su amfana, Tribune ta rahoto.

Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin Bauchi karƙashin jagorancinsa za ta shiga kasuwanci kala daban-daban kuma ba za ta bari yarjejeniyar gina kamfanin ta tafi a banza ba.

Yaushe za a fara aikin simintin a Bauchi:?

Kara karanta wannan

Ana shirin gama zanga zanga, gwamna ya sake daukar sabon mataki

Shugaban Resident Cement Factory Limited, Junaid Waziri, ya ce hadin gwiwar zai ba kamfanin damar ci gaba da aikin, kuma za a fara aikin ne a farkon 2025.

Waziri ya yabawa jagoranci da jajircewar Gwamna Bala wajen kawo ci gaba a Bauchi, inda ya ce za su gina masana'antar da zata fitar da tan miliyan 10 na siminti.

Wani mai sana'ar sayar da siminti a Ɗanja ya shaidawa Legit Hausa cewa hanya ɗaya za a iya sauke farashin siminti a kasuwa a yanzu, kuma ita ce yawansa ya fi buƙatarsa.

Dilan mai suna Malam Lawal ya ce har yanzu yadda mutane ke bukatar siminti, ya fi yawan wanda suke kawowa kasuwa, shiyasa da wahala farashin ya yi ƙasa.

"Mangal ya fara, yanzu ga wannan da Bauchi za su fara, ina ganin idan da gwamnati za ta fahimta, ta buɗe boda a riƙa shigowa da siminti, ta haka za a samu sauki.

Kara karanta wannan

Shekarau ya fadi dalilinsa na kin tsoma baki a rikicin masarautar Kano

"A halin yanzu N7,000 muke sayar da buhu a nan Ɗanja, kuma ban sani ba ko a nan ne kaɗai amma idan ya kare mutane za su dinga zuwa nema tun kafin a kawo mana.
"Amma idan yau aka ce duk neman da za a yi ba za a rasa siminti ba, wataƙila farashin ya sauka amma a tunani ne kenan, Allah ya kawo mana sauƙi a ƙasar nan," in ji shi.

Sanata Bala ya kori hadiminsa a Bauchi

A wani rahoton kuma gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya sallami babban mai ba shi shawara kan harkokin tsaro daga kan muƙaminsa.

Gwamna Bala Mohammed ya kori Ahmed Chiroma ne daga kan muƙaminsa a ranar Talata, 16 ga watan Yulin 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262