Zanga Zanga: Gwamna Ya Tsausaya Wa Mutanen Kaduna da Zaria, Ya Ɗauki Sabon Mataki
- Gwamna Malam Uba Sani ya sassauta dokar hana zirga-zirga da gwamnatinsa ta sanya a cikin Kaduna da Zariya
- Kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwa ya ce daga yanzu mutane na da damar gudanar da harkokinsu daga karfe 8:00 na safe zuwa 6:00 na yamma
- Ya ce dokar za ta fara aiki daga 6:00 na yamma zuwa 8 na safe kuma jami'an tsaro za su ci gaba da sa ido kan yadda al'amura ke tafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kaduna - Gwamna Malam Uba Sani ya tausayawa mutane, ya sassauta dokar hana fita ta tsawon sa'o'i 24 da aka sanya a birnin Kaduna da Zariya.
Gwamnan ya sassauta dokar, inda ya bai wa al'umma damar fita su gudanar da harkokinsu na yau da kullum daga ƙarfe 8:00 na safe zuwa 6:00 na yamma.
Gwamnatin Kaduna ta sassauta doka
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Laraba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce daga yanzu dokar hana fita za ta fara aiki daga ƙarfe 6:00 na yammacin kowace rana zuwa ƙarfe 8:00 na safe a cikin Kaduna da Zariya.
Kwamishinan ya ce an ɗauki matakin sassauta dokar kullen ne a taron majalisar tsaro ƙarƙashin jagorancin Gwamna Uba Sani.
Dalilin halatta fita a Kaduna, Zariya
Aruwan ya bayyana cewa majalisar ta yi nazari sosai kan yadda al'amura ke tafiya, don haka ta amince da sassauta dokar hana fita da ta kafa tun a ranar Litinin 4 ga watan Agusta 2024.
A cewarsa, Majalisar Tsaron Kaduna ta lura cewa abubuwa sun fara dawowa daidai a Kaduna da Zaria, shiyasa ta amince da sassauta dokar da ta sanya.
Ƴan sandan Kaduna za su ɗauki mataki
Bugu da ƙari, jami'an tsaro za su ci gaba da sa ido don ganin dokar tana aiki daga karfe 6:00 na yamma zuwa 8:00 na safiya.
Haka nam kuma jami'an tsaron sun shirya ɗaukar mataki kan duk wani abu da suka ga zai iya kawo tashin hankali da karya doka da oda a lokacin da mutane ke zirga-zirga.
Wani mai shagon kayan wuta, Suleiman Abdullahi ya shaidawa Legit Hausa cewa sun samu fita kasuwa yau Alhamis.
Ya ce abin da ya faru a lokacin zanga-zanga musamman a Samaru babu daɗi amma a zahirin gaskiya wasu ne suka jawo ma wasu.
"An bar mu mun fita kasuwa yau, ban ga laifin gwamnati ba da ta sa wannan doka duba da yadda zanga zanga ta rikiɗa ta koma tashin hankali har da kisa. Muna fatan karshen abun kenan," in ji Suleiman.
Matasa sun kona fadar hakimi a Bauchi
A wani rahoton kuma matasa sun ƙona fadar Hakimin Lere da ke ƙaramar hukumar Tafawa Ɓalewa a jihar Bauchi bayan kisan ɗan uwansu matashi.
Mazauna yankin sun bayyana cewa matasan sun huce fushinsu kan hakimin ne bisa zargin shi ya ƙarfafawa sojoji guiwa su sanya dokar hana fita.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng