Shugaban NOA Ya Faɗi Matsalar da Za a Shiga Idan Aka Dawo da Tallafin Fetur
- Darakta Janar na hukumar wayar da kan al'umma ya ce dawo da tallafin fetur ba zai yaye wa mutane talaucin da ake ciki ba
- Lanre Issa-Onilu ya buƙaci ƴan Najeriya su lalubo dabarun da za su taimaka masu a rayuwa bayan tuge tallafin man fetur
- Maido da tallafin na ɗaya daga cikin manyan buƙatun masu zanga-zanga wanda tuni shugaban ƙasa ya ce ba zai yiwu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Darakta-Janar na hukumar wayar da kan jama’a ta kasa (NOA), Lanre Issa-Onilu, ya yi fatali da baƙatar dawo da tallafin man fetur a Najeriya.
Issa-Onilu ya bayyana cewa dawo da tallafin ba zai warware wahalar da ake ciki ba illa ya ƙara jefa mutane cikin baƙin talauci.
Tinubu ya kore dawo da tallafin fetur
Daya daga cikin bukatun masu zanga-zangar adawa da manufofin gwamnati mai ci shi ne a dawo da tallafin man fetur wanda shugaban ƙasa Bola Tinubu ya tuge tun ranar farko.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daily Trust ta ce a jawabin da ya yi ranar Lahadi, Shugaba Bola Tinubu ya kore yiwuwar mayar da tallafin, yana mai cewa cire shi yana da zafi amma ya zama dole.
Matsalar dawo da tallafin man fetur
Da yake jawabi a Sunrise Daily, shirin safe na Channels tv ranar Laraba, Issa-Onilu ya shawarci 'yan Najeriya da su tsara dabarun rayuwa bayan cire tallafin mai.
Daraktan NOA ya ce:
"Duk wanda ka ji ya bukaci a dawo da tallafin man fetur, ya yi haka ne don son ransa amma ba wai don amfanin tattalin arziki ba.
"Saboda haka idan kuna bukatar a dawo da shi sai kun gamsar da mu cewa hakan zai magance talauci. Ba zai warkar da mutane ba sai dai ya kara jefa su a bakin talauci."
Daraktan NOA ya ƙara da cewa babbar matsalar da ake samu tsakanin mabiya da shugabanni ta samo asali ne daga rashin cika alƙawurra na tsawon shekaru.
Hafsoshin tsaron ECOWAS sun gana a Abuja
Kuna da labarin hafsoshin tsaro na ƙasashen ƙungiyar ECOWAS sun gana a birnin tarayya Abuja karkashin jagorancin Janar Christopher Musa.
Taron wanda ya gudana a hedkwatar tsaro ta kasa ya samu halartar duka hafsoshin tsaron kasashen yammacin Afirka ban da na ƙasashe uku.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng