Zanga Zanga: Manyan Hafoshin Sojin Kasashen ECOWAS Sun Shiga Ganawa a Abuja

Zanga Zanga: Manyan Hafoshin Sojin Kasashen ECOWAS Sun Shiga Ganawa a Abuja

  • Hafsoshin tsaro na ƙasashen ƙungiyar ECOWAS sun gana a birnin tarayya Abuja karkashin jagorancin Janar Christopher Musa
  • Taron wanda ya gudana a hedkwatar tsaro ta kasa ya samu halartar duka hafsoshin tsaron kasashen yammacin Afirka ban da na ƙasashe uku
  • Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ministan tsaro, Abubakar Badaru da ministan harkokin waje, Yusuf Tuggar sun halarci taron

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Manyan hafsoshin soji na kasashen da ke ƙarƙashin ƙungiyar ECOWAS na ganawa yanzu haka a hedkwatar tsaro ta ƙasa da ke birnin tarayya Abuja.

Wannan taro na zuwa ne a lokacin da ƴan Najeriya ke gudanar zanga-zanga kan tsadar rayuwa, inda wasu ke ta kiraye-kirayen sojoji su karɓe mulkin Najeriya.

Kara karanta wannan

Farfesa ya tona ainihin Masu ɗaga tutocin ƙasar Rasha wajen zanga zanga

Janar Christopher Musa.
Hafsoshin sojin ƙasashen yammacin Afirka sun sa labule a Abuja Hoto: Depence Headquaters Nigeria
Asali: Facebook

Tuni dai babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Chirstpher Musa ya yi fatali da kiran hamɓarar da gwamnatin demokuradiyya, kamar yadda The Nation ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Taron dai na gudana ne karkashin jagorancin babban hafsan hafsoshin Najeriya, Janar Christopher Musa, wanda shi ne shugaban kwamitin hafsoshin tsaro na ECOWAS.

Hafoshin tsaron da suka halarci taron

Waɗanda suka halarci taron sun haɗa da babban hafsan hafsoshin tsaro, CDS Christopher Musa, da kuma manyan hafsoshin tsaron kasashen yammacin Afirka ban da na Mali, Burkina Faso da Nijar.

Ministan tsaron Najeriya, Mohammed Abubakar Badaru, ministan harkokin waje Yusuf Tuggar da mai ba da shawara kan tsaron ƙasa (NSA), Nuhu Ribadu sun halarci taron.

Hat ila yau taron wanda ke gudana yanzu haka a Abuja ya samu halartar shugaban kwamitin tsaro na majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan da takwaransa na majalisar wakilai.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Abin da Tinubu ya faɗawa hafsoshin tsaro kan masu ɗaga tutar Rasha

Zanga-zanga: Sojoji sun shirya ɗaukar mataki

A wani labarin kun ji cewa babban hafsan hafsoshin tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya ce sojoji za su shiga tsakani idan masu zanga zanga suka ci gaba da keta doka

Janar Christopher Musa ya bayyana cewa idan suka fahimci lamarin ya sha kan jami'an ƴan sanda, za su kawo ɗauki domin tabbatar da zaman lafiya a ƙasar nan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262