Matasa Sun Yanke Shawara, Sun Dakatar da Zanga Zanga Saboda Babban Bikin Al'ada

Matasa Sun Yanke Shawara, Sun Dakatar da Zanga Zanga Saboda Babban Bikin Al'ada

  • Masu zanga zanga sun dakatar da ita saboda matsowar bikin al'adun Osogbo na wannan shekarar 2024 a jihar Osun
  • Matasan sun mika takardar bukatursu ga mataimakin gwamna kuma an masu alkawarin cewa za ta isa ofishin shugaban ƙasa
  • Wannan na zuwa ne kwanaki shida bayan fara zanga-zangar adawa da manufofin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Osun - Matasa sun dakatar da zanga-zangar da suke yi a jihar Osun da ke Kudu maso Yamma saboda bikin al'ada na Osun-Osogbo da ke tafe a 2024.

Masu zanga-zangar sun ɗauki wannan matakin ne bayan miƙa takardar ƙorafe-ƙorafen su ga Gwamna Ademola Adeleke a fadar gwamnatin Osun da ke Osogbo.

Kara karanta wannan

Rana ta 5: Zanga zanga ta ɗauki sabon salo, wasu matasa sun yi tsirara a kan titi

Matasan Najeriya.
An dakatar da zanga-zanga a jihar Osun saboda zuwan bikin al'adun Osogbo Hoto
Asali: Getty Images

Zanga-zanga ta zo karshe a jihar Osun

Mataimakin gwamna, Kola Adewusi shi ya karɓi takardar a madadin mai girma gwamna, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Adewusi ya tabbatar wa masu zanga-zangar cewa gwamnan zai mika wasikar ga shugaban kasa Bola Tinubu hannu da hannu, don haka su ɗauka sakonsu ya isa.

Da suke zantawa da manema labarai a sakatariyar NUJ da ke Osogbo, masu zanga-zanga a jihar Osun sun bayyana cewa sun dakatar da zanga-zanga gaba ɗaya.

Meyasa aka dakatar da zanga-zanga a Osun?

A ruwayar Vanguard, jagoran tawagar masu zanga-zangar, Kwamared Adetunji Ajala ya ce:

"Mu da muka jagoranci shirya wannan zanga-zanga a jihar Osun muna sanar da al'umma cewa tun da muka fara zanga-zanga ga shi yau muna rana ta shida, mun faɗi koken mu a fili.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: An kama mutumin da ke ɗinka tutocin ƙasar Rasha a jihar Kano

"Muna bukatar shugabanninmu a kasar nan su gaggauta shawo kan wahalar rayuwa da ta addabi ƴan Najeriya. Mun ji jawabin shugaban ƙasa amma gaskiya ba mu ji daɗi ba."
"Duk da haka mun miƙa buƙatunmu ga gwamnan Osun kuma ya uo mana alƙawarin za a duba."
"Bisa la'akari da yanayin tsaro da bikin al'adar Osogbo da ke tafe, mun dakatar da zanga-zanga daga yau 6 ga watan Agusta."

Yan daba sun farmaki hedkwatar APC

A wani rahoton kuma masu zanga-zanga da ake zargin ƴan daba ne sun yi kaca-kaca da sakatariyar APC da ke titin Fatakwal zuwa Aba a jihar Ribas.

Mukaddashin shugaban APC na jihar Ribas, Cif Tony Okocha ya ce sun san waɗanda suka ɗauki nauyin wannan aika-aika da aka yi masu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262