Gwamna Ya Gama Shiri, Zai Fara Biyan Ma'aikata Sabon Albashi Ana Tsaka da Zanga Zanga
- Gwamna Abdullahi Sule ya ce nan ba da jimawa ba ma'aikatan gwamnati za su fara shan romon sabon mafi karancin albashi a Nasarawa
- Abdullahi Sule ya bayyana cewa tuni ya gama shirin fara biyan N70,000 bayan shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya rattaɓa hannu a dokar
- Mai girma Gwamnan ya kuma tabbatarwa al'ummar cewa ba zai kyale duk wani jami'in gwamnati da aka kama da rashin gaskiya ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Nasarawa - Gwamna Abdullahi Sule ya ce ya gama shirin fara biyan N70,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi ga ma’aikatan gwamnati a jihar Nasarawa.
Mai magana da yawun gwamnan, Kwamared Peter Ahemba ne ya bayyana haka a wata hira da manema labarai.
Yaushe Gwamnan zai fara biyan sabon albashi?
Ahemba ya bayyana cewa tuni Gwamna Sule ya amince da biyan sabon mafi karancin albashin wanda za a fara nan ba da dadewa ba a jihar Nasarawa, Vanguard ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Gwamna Abdullahi Sule ya gama shirin fara biyan mafi karancin albashi na ₦70,000 wanda shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya rattaɓawa hannu ya zama doka.
"Mai girma Injiniya Sule ya himmatu wajen kyautata jin dadin ma’aikata da kuma ci gaban jihar baki daya,” in ji Ahemba.
Gwamna Sule ya yabawa matasan Nasarawa
Ahemba ya ce gwamnan ya yaba wa matasan Nasarawa kan yadda suka kaucewa shiga zanga-zangar da ake yi a ƙasar nan, maimakon haka suka zaɓi tattaunawa.
Ya ce Gwamnatin Abdullahi Sule tana sane da irin wahalhalun da mutane ke ciki a halin yanzu, kuma tana daukar matakai don magance su, rahoton Guardian.
Daga ƙarshe Gwamna Sule ya bukaci matasan da su kwantar da hankulan su domin gwamnatinsa na aiki tukuru don samar da ayyukan yi ta hanyoyi da dama.
Gwamnan Ebonyi zai rabawa matasa N1.3bn
Kuna da labarin Gwamnan jihar Ebonyi ya nuna farin ciki bisa yadda matasa suka yi masa biyayya, suka ƙi shiga zanga-zangar da aka fara.
Francis Nwifuru ya bayyana cewa gwamnati ta ware N1.3bn domin rabawa matasa 1,300 tallafin da za su kama sana'a su dogara da kansu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng