Zanga Zanga: Jami'an DSS Sun Kama Masu Ɗaukar Nauyin Telolin Tutar Rasha a Kano
- Jami'an hukumar tsaron farin kaya DSS sun cafke masu ɗaukar nauyin telolin tutar ƙasar Rasha a jihar Kano da ke Arewa maso Yamma
- Tun farko dai jami'an tsaron sun kama telolin da ke ɗinka tutar a ranar Litinin bayan masu zanga-zanga sun fara ɗaga tutocin a kan titi
- Gwamnatin Rasha ta bakin ofishin jakadancin ƙasar a Najeriya ta musanta hannu a zanga zangar da ake yi a sassan Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta ce jami’anta sun kama wasu teloli da ke dinkawa masu zanga zanga tutocin kasar Rasha a Kano.
Hukumar DSS ta ce jami’anta sun kuma kama masu daukar nauyin telolin da ke ɗinka tutocin yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike.
Hakan na kunshe ne a wata gajeruwar sanarwa da DSS ta wallafa a shafinta na manhajar X wanda aka fi sani da Tuwita ranar Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jami'an DSS sun kama shugaban matasa?
Rundunar ‘yan sandan sirrin ta musanta cewa tana tsare da Adaramoye Michael, kodinetan kungiyar matasa (YRC), ta ce shugaban matasan bai hannunta.
"Hukumar DSS na ta iya tabbatarwa al'umma da cewa ba ta kama Adaramoye Michael (wanda aka fi sani da Michael Lenin) ba."
DSS ta kama telolin tutar kasar Rasha
Hukumar DSS ta kuma tabbatar da cewa bayan kama telolin da ke ɗinka tutocin Rasha a Kano, jami'anta sun gano tare da cafke masu ɗaukar nauyinsu.
"Hukumar ta kama wasu teloli a jihar Kano masu ɗinka tutocin kasar Rasha da ake rabawa masu zanga zanga. Wasu daga cikin masu ɗaukar nauyinsu sun shiga hannu," in ji DSS.
A ranar Alhamis, 1 ga watan Agusta, 2024 matasa suka fara zanga-zanga ta tsawon kwanaki 10 mai taken ‘EndBadGovernance’ a sassa da dama na kasar nan.
Masu zanga-zanga sun farmaki sakatariyar APC
A wani rahoton kun ji cewa masu zanga-zanga sun farmaki hedkwatar jam'iyyar APC reshen jihar Zamfara ranar Litinin, 5 ga watan Agusta, 2024.
Sakataren yaɗa labarai na APC a jihar, Yusuf Idris ya ce ɓata garin sun lalata muhimman kayayyakin da ke ajiye a ofisoshi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng