Rana Ta 5: Zanga Zanga Ta Ɗauki Sabon Salo, Wasu Matasa Sun Yi Tsirara a Kan Titi

Rana Ta 5: Zanga Zanga Ta Ɗauki Sabon Salo, Wasu Matasa Sun Yi Tsirara a Kan Titi

  • Zanga-zanga ta ɗauki sabon salo a rana ta biyar yayin da wasu matasa suka cire tufafin su gaba ɗaya saboda halin kuncin da ake ciki
  • Rahotanni sun bayyana cewa wasu daga cikin masu zanga zangar sun cire kayansu ne yayin da suke kokawa kan kunyar da Tinubu ya ba su
  • Wannan na zuwa ne bayan shugaban kasa ya bada umarnin ɗaukar mataki kan masu ɗaga tutar kasar waje a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Osun - Zanga-zangar yunwa da ake yi a faɗin Najeriya ta ɗauki sabon salo ranar Litinin, 5 ga watan Agusta, 2024.

Rahotanni sun bayyana cewa wasu daga cikin masu zanga-zanga sun tube tufafinsu, sun yi tsirara haihuwar uwa domin nuna takaicinsu kan halin da ake ciki a jihar Osun.

Kara karanta wannan

Kasar Rasha ta yi magana kan masu zanga zangar da ke ɗaga tutocinta a Najeriya

Masu zanga zanga.
Wasu daga cikin masu zanga zanga sun yi tsirara a jihar Osun Hoto: @Aliyussufiy
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa tun da aka fara zanga-zangar, matasa kan taru a wurin shaƙatawa na Freedom a kowace rana, sannan su zagaye cikin gari.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sun jaddada cewa ba za su dakatar da zanga-zanga ba har sai shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ɗauki matakin rage raɗaɗin da ƴan Najeriya ke ciki.

Yadda zanga-zanga ta gudana a Osun

Da safiyar yau Litinin, rana ta biyar da fara zanga zanga, matasan sun sake taruwa a wurin shaƙatawar kamar yadda suka saba.

Masu zanga-zangar sun yi tattaki daga filin shakatawa na Freedom zuwa Ajegunle, Olonkoro, Igbona, Ayetoro, sannan suka koma mahadar Olaiya inda shugabanninsu suka yi musu jawabi.

Masu zanga-zanga sun yi cire tufafi

Sai dai anyi wata ƴar dirama a lokacin zanga zangar yayin da wasu daga cikin matasan suka sabule tufafinsu, suka yi tsirara a kan titi, Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Zanga zanga ta birkice, matasa sun toshe hanyoyi

Matasan sun yi tsirara ne daidai lokacin da suke kokawa cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ba su kunya bayan sun kaɗa masa ƙuri'unsu.

Masu zanga-zangar dai sun ce ba za su ja da baya ba har sai shugaban kasar ya fito da kwakkwaran mataki na rage radadin da ake fama da shi a Najeriya.

Tinubu ya umarci kama masu ɗaga tutar Rasha

A wani rahoton kuma Bola Ahmed Tinubu ya umarci jami'an tsaro su ɗauki mataki kan duk wanda suka gani ɗauke da tutar Rasha ko wata kasar ƙetare

Babban hafsan tsaro na ƙasa, Janar Christopher Musa ne ya bayyana haka a Aso Villa jim kaɗan bayan taron majalisar tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262