Zanga Zanga: Abin da Tinubu Ya Faɗawa Hafsoshin Tsaro kan Masu Ɗaga Tutar Rasha

Zanga Zanga: Abin da Tinubu Ya Faɗawa Hafsoshin Tsaro kan Masu Ɗaga Tutar Rasha

  • Bola Ahmed Tinubu ya umarci jami'an tsaro su ɗauki mataki kan duk wanda suka gani ɗauke da tutar Rasha ko wata kasar ƙetare
  • Babban hafsan tsaro na ƙasa, Janar Christopher Musa ne ya bayyana haka a Aso Villa jim kaɗan bayan taron majalisar tsaro
  • Ya ce ɗaga tutar wata ƙasa a cikin Najeriya laifi ne na cin amana kuma duk wanda aka kama zai ɗanɗana kuɗarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci jami'an tsaro su cafke duk wanda suka gani ɗauke da tutar ƙasar Rasha a Najeriya.

Babban hafsan sojojin Najeriya (CDS), Janar Christopher Musa ne ya bayyana haka yayin hira da ƴan jarida bayan taron majalisar tsaro a Aso Villa yau Litinin.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Sojojin Najeriya sun yi magana kan kifar da gwamnatin Bola Tinubu

Babban hafsan tsaro, Janar Christopher Musa.
Shugaba Tinubu ya bada umarnin cafke masu ɗaga tutocin Rasha a Najeriya Hoto: Defence HQ Nigeria
Asali: Facebook

Hafoshin tsaro sun yiwa Tinubu bayani

Ya ce hafsoshin tsaro sun yi wa shugaban kasa bayanin halin da ake ciki game da tsaro a ƙasar nan a taron, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Janar Musa ya ce shugaban kasa na bukatar ya san meke faruwa duba da zanga-zangar da ake ci gaba da yi, wacce ta rikiɗa ta zama tashin hankali a wasu jihohin.

Ya ce lamarin ya kara dagulewa ne yayin da masu zanga-zangar suka fara ɗaga tutocin kasashen waje a cikin Najeriya, wanda ba zai yiwu a bar haka ya ci gaba ba.

Wane mataki Bola Tinubu ya ɗauka?

Daily Trust ta rahoton Janar Musa na cewa:

"Muna yi muku kashedi da babbar murya kuma shugaban kasa ya ce mu sanar da ku cewa ba za mu ƙyale duk wani mutumi da ya ɗaga tutar wata ƙasa a cikin Najeriya ba.

Kara karanta wannan

Kasar Rasha ta yi magana kan masu zanga zangar da ke ɗaga tutocinta a Najeriya

"Wannan laifi ne na cin amanar kasa, kuma za mu ɗauki mataki domin hukunta mai laifi daidai da abinda ya aikata. Don haka, kada wanda ya yarda wani ya yi amfani da shi,” in ji shi.

Christopher Musa ya yi zargin cewa galibi ƙananan yara ake sa wa su ɗaga tutocin wata ƙasa kuma jami'an tsaro ba za su zuba ido suna kallo ba.

Sojoji zasu kare dimokuraɗiyya

Kun ji cewa babban hafsan sojojin Najeriya ya ce ba za su lamunci duk wani yunkuri na canza gwamnati ta hanyar fakewa da zanga-zanga ba.

Janar Christopher Musa ya ce Najeriya ƙasa ce mai bin tsarin demokuraɗiyya kuma jami'an tsaro a shirye suke su ba ta kariya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262