Zanga Zanga: Sojojin Najeriya Sun Yi Magana Kan Kifar da Gwamnatin Bola Tinubu

Zanga Zanga: Sojojin Najeriya Sun Yi Magana Kan Kifar da Gwamnatin Bola Tinubu

  • Babban hafsan sojojin Najeriya ya ce ba za su lamunci duk wani yunkuri na hamɓarar gwamnati ta hanyar fakewa da zanga-zanga ba
  • Janar Christopher Musa ya ce Najeriya ƙasa ce mai bin tsarin demokuraɗiyya kuma jami'an tsaro a shirye suke su ba ta kariya
  • Ya bayyana haka ne yayin zantawa da manema labarai a fadar shugaban ƙasa jim kaɗan bayan ganawa da Bola Tonubu ranar Litinin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Rundunar sojojin Najeriya ta bayyana cewa ba za ta lamunci duk wani yunƙuri na amfani da zanga-zangar da ake yi wajen kifar da gwamnatin ƙasar nan ba.

Babban hafsan hafsoshin sojin Najeriya (CDS), Janar Christopher Musa ne ya bayyana haka yayin hira da masu ɗauko rahoto a fadar shugaban kasa yau Litinin.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Abin da Tinubu ya faɗawa hafsoshin tsaro kan masu ɗaga tutar Rasha

Christopher Musa.
Babban hafsan tsaro ya kore yiwuwar sauya gwamnatin Najeriya Hoto: Defence HQ Nigeria
Asali: Facebook

Sojoji ba su yarda da canza gwamnati ba

Janar Musa ya ce sojoji za su yi duk mai yiwuwa wajen daƙile yunƙurin hamɓarar da gwamnati da sunan zanga-zanga, Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hafsan tsaron ya ce shugaban ƙasa ya fito fili ya sanar da cewa gwamnati ba za ta ƙyale duk wanda ke son kawo cikas ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya ba.

Ya kuma yi fatali da ɗaga tutar kasar waje a Najeriya, yana mai cewa irin wannan aikin cin amanar kasa ne, kamar yadda The Nation ta kawo.

Jami'an tsaro zasu kare gwamnatin dimokuraɗiyya

"Da farko lokacin da aka fara sun ce zanga-zangar lumana ce, amma daga bisani muka fahimci cewa akwai wasu mutane da suke son yin amfani da ita don ta da tarzoma."

Kara karanta wannan

Babban hafsan tsaro ya fadi laifin masu daga tutar Rasha, ya gargadi 'yan zanga zanga

"Kowa ya ga abin da ya faru tun bayan fara zanga-zangar, ɓata gari sun karɓe ta suna sace-sace, ƙone-ƙone da sauransu."
"Najeriya kasa ce mai bin tafarkin dimokuradiyya kuma jami'an tsaro da za su kare tsarin mulki."
"Ba za mu kyale duk wanda ke ƙoƙarin ganin an kifar da gwamnati ba. A kan tsarin demokuraɗiyya muke kuma zamu ci gaba da kare ta."

- Shugaban hafsun tsaro, Janar C. Musa.

Rasha ta yi magana kan ɗaga tutocinta

Ku na da labarin kasar Rasha ta musanta raɗe-raɗin cewa tana da hannu a ɗaga tutocin da matasa masu zanga-zanga ke yi a Najeriya.

Ofishin jakadancin Rasha a Najeriya ya ce gwamnatin Shugaba Putin ba ta sa baki a harkokin cikin gida na kowace ƙasa a duniya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262