Kasar Rasha Ta Yi Magana Kan Masu Zanga Zangar da ke Ɗaga Tutocinta a Najeriya
- Ƙasar Rasha ta musanta raɗe-raɗin cewa tana da hannu a ɗaga tutocin da matasa masu zanga-zanga ke yi a Najeriya
- Ofishin jakadancin Rasha a Najeriya ya ce gwamnatin Shugaba Putin ba ta sa baki a harkokin cikin gida na kowace ƙasa a duniya
- Wannan na zuwa ne a lokacin da masu zanga-zangar adawa da manufofin gwamnatin Bola Tinubu suka fara ɗaga tutar Rasha musamman a Arewa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Ƙasar Rasha ta musanta cewa tana da hannu a ɗinkawa da ɗaga tutocin ƙasar da wasu masu zanga-zanga ke yi a Arewacin Najeriya.
Ofishin jakadancin Rasha a Najeriya ne ya bayyana haka, ya ce ko kaɗan ba su da hannu a tawagar matasan da aka ga suna ɗaga tutocin Rasha yayin da suka fito zanga-zanga.
Daily Trust ta tattaro cewa masu zanga-zanga a wasu jihohi sun fito kan tituna ɗauke da tutocin kasar Rasha kuma suna rera taken ƙasar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana dai zargin Rasha, ƙasa mai karfin fada a ji a duniya da hannu a rikice-rikicen siyasa na baya-bayan nan a wasu kasashen yammacin Afirka da suka hada da Mali, Burkina Faso, da Nijar.
Zanga-zanga: A karshe Rasha ta magantu
A wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, ofishin jakadancin ya jaddada cewa Rasha ba ta tsoma baki cikin harkokin wasu kasashe ciki har da Najeriya.
"Mun lura da wasu rahotannin da kafafen yada labarai na Najeriya ke yadawa da bidiyo da hotuna da ke nuna masu zanga-zanga dauke da tutocin Rasha suna rera taken shugaban Rasha Vladimir Putin.
"Gwamnatin Rasha da jami'anta ba su da hannu ko kaɗan a lamarin kuma ba ta da alaƙa da su. Kamar kowane lokaci muna kara jaddada cewa Rasha ba ta tsoma baki a harkokin ƙasashe ciki har da Najeriya."
Sanarwar ta ƙara da cewa Rasha na mutunta tsarin demokuraɗyyar Najeriya kuma tana Allah wadai da duk wani abu da zai haifar da tashin-tashina a ƙasar nan, rahoton The Nation.
Ƴan sanda sun kama telan tutocin Rasha
A wani rahoton kuma jami'an tsaro sun kama wani tela mai suna Ahmed bisa zarginsa da yaɗa tutocin ƙasar Rasha a jihar Kano a lokacin zanga-zanga.
Rahotanni sun nuna matasa sun fara ɗaga tutocin ƙasar ketaren ne a makon da ya wuce, amma lamarin ya ƙara yaɗuwa a ranar Litinin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng