Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Manyan Hafsoshin Tsaro Ana Tsaka da Zanga Zanga

Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Manyan Hafsoshin Tsaro Ana Tsaka da Zanga Zanga

  • Bola Ahmed Tinubu ya shiga ganawa da hafsoshin tsaro a fadar shugaban ƙasa da ke babban birnin tarayya Abuja ana tsaka da zanga zanga
  • Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima da shugaban ma'aikatan fadar gwamnati Femi Gabajabiamila sun halarci taron yau Litinin
  • Wannan taro na zuwa ne sa'o'i 24 bayan Bola Tinubu ya ce ba zai zuba ido yana kallo wasu tsiraru su ruguza Najeriya ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu na ganawar sirri yanzu haka da manyan hafsoshin tsaron ƙasar nan a Aso Villa da ke birnin tarayya Abuja.

Taron dai na gudana ne karkashin majalisar tsaro ta Najeriya a fadar shugaban ƙasa yau Litinin, 5 ga watan Agusta, 2024 yayin da ake tsaka da zanga-zanga.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Abin da Tinubu ya faɗawa hafsoshin tsaro kan masu ɗaga tutar Rasha

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Bola Tinubu ya shiga ganawa da hafsoshin tsaro a fadar shugaban ƙasa Hoto: Ajuri Ngelale
Asali: Facebook

Babban hafsan tsaro na ƙasa, Janar Christopher Musa ne ya jagoranci hafsoshin tsaro da sauran shugabannin hukumomin tsaro zuwa taron, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da matasa ke ci gaba da gudanar da zanga-zangar adawa manufofin gwamnatin Tinubu da suka kawo yunwa a kasar.

Tinubu ya yi jawabi ga ƴan Najeriya

A jiya Lahadi, shugaban ƙasa ya yi jawabi kai tsaye ga ƴan Najeriya kan halin da ake ciki, inda ya buƙaci a dakatar da zanga-zangar da aka fara.

Bola Tinubu ya bayyana cewa ba zai zauna ya naɗe ƙafa yana kallon wasu tsiraru da ƴan adawa suka ɗauko haya su ruguza zaman lafiya ba.

Ya kuma tabbatarwa masu zanga zangar cewa ya ji duka kokensu tare da gargaɗin cewa ba zai bari a ci gaba da asarar rayuwa da dukiyoyi ba.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Sojojin Najeriya sun yi magana kan kifar da gwamnatin Bola Tinubu

Bola Tinubu na ganawa da shugabannin tsaro

A halin yanzu dai mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima da shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila sun halarci taron tsaron yau Litinin.

Sauran mahalarta taron sun haɗa da Sufeto Janar na rundunar ƴan sanda, IGP Kayode Egbetokun da sauran shugabannin hukumomin tsaro, Daily Trust ta rahoto.

Ministan Buhari ya soki jawabin Tinubu

A wani rahoton kuma tsohon ministan matasa da wasanni ya mayar da martani kan jawabin da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi ranar Lahadi.

Solomon Dalung ya bayyana cewa jawabin shugaban kasar bai da alaƙa da ƴan Najeriya don haka za su ci gaba da zanga-zanga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262