Wani Malamin Addini Ya Gayawa Tinubu Gaskiya, Ya Fadi Babbar Matsalar Gwamnatinsa

Wani Malamin Addini Ya Gayawa Tinubu Gaskiya, Ya Fadi Babbar Matsalar Gwamnatinsa

  • Primate Elijah Ayodele ya gano matsalar gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu wacce ta kwashe shekara ɗaya da ƴan watanni a kan mulki
  • Babban faston ya bayyana cewa ministoci da hadimansa su ne babbar matsalar gwamnatinsa domin ba su taɓuka abin kirki
  • Ya yi gargaɗin cewa idan aka ci gaba da zanga-zangar da ake yi a faɗin ƙasar nan, abubuwa za su taɓarɓare

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Legas - Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Primate Elijah Ayodele, ya ba shugaban ƙasa Bola Tinubu, shawara.

Babban malamin addinin ya shawarci Shugaba Tinubu da ya kori ministoci da hadimansa saboda suna da matsala ga gwamnatinsa.

Primate Ayodele ya ba Tinubu shawara
Primate Ayodele ya bukaci Tinubu ya kori ministocinsa Hoto: Primate Elijah Ayodele, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Fasto Ayodele ya ba Tinubu shawara

Primate Elijah Ayodele ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Osho Oluwatosin ya sanyawa hannu, cewar rahoton jaridar PM News.

Kara karanta wannan

Babban lauya ya ba Tinubu lakanin kawo karshen zanga zangar da ake yi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Babban faston ya ce zanga-zangar da ake yi ba domin Tinubu ba ne kaɗai, amma rashin nagartar ministoci da muƙarrabansa ya taimaka matuƙa wajen gudanar da zanga-zangar.

Ya bayyana cewa ana shan wuya a ƙasar nan kuma abin da Tinubu ya kamata ya yi shi ne rage farashin kayan abinci da man fetur da wutar lantarki domin hana ƴan Najeriya ƙorafi, rahoton Daily Post ya tabbatar.

Me Ayodele ya ce kan zanga-zanga?

Primate Ayodele ya ce idan aka ci gaba da zanga-zangar, ƙasar nan za ta ruguje.

Ya kuma yi nuni da cewa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, babbar matsala ce ga Shugaba Tinubu.

"Ana shan wuya a ƙasar nan, ya kamata ya rage farashin kayan abinci, wuta da man fetur, zai ga mutane ba za su damu da komai ba."

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya yi magana a karon farko bayan fara zanga zanga a Najeriya

"Suna izgili ga gwamnatinsa, sannan ministocinsa ba sa taimaka masa. Hatta shugaban majalisar dattawa matsala ce ga gwamnatinsa saboda bai jagoranci mai kyau, da yana yi da ba a samu wannan zanga-zangar ba."
"Idan aka ci gaba da wannan zanga-zangar, za ta ɓata wannan gwamnatin, abin da kawai yake buƙata shi ne ya inganta wutar lantarki, man fetur da abinci amma ya yi kunnen uwar shegu."
"Ina tunanin akwai wani abu dangane da wannan kujerar da yake sanyawa shugabannin ƙasa su zama kurame."

- Primate Elijah Babatunde Ayodele

Tinubu ya magantu kan zanga-zanga

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatinsa na daukar kwararan matakai don farfaɗo da tattalin arzikin Najeriya wanda ya durkushe.

Ya kuma buƙaci ƙasashen Afirka su fito su haɗa karfi da ƙarfe su tunkari duk wata gargada da ta tare masu tattalin arziki kuma kada su yi wasa da kowace irin dama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng