Shugaba Tinubu Ya Yi Magana a Karon Farko Bayan Fara Zanga Zanga a Najeriya

Shugaba Tinubu Ya Yi Magana a Karon Farko Bayan Fara Zanga Zanga a Najeriya

  • Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatinsa na ɗaukar matakai masu tsauri da nufin farfaɗo da tattalin arzikin Najeriya
  • Shugaban ƙasar ya faɗi haka ne ranar Jumu'a a Abuja a lokacin da ƴan Najeriya suka shiga rana ta biyu a zanga-zangar da suka fara
  • Shugaba Tinubu ya buƙaci kasashen Afirka su haɗa karfi da karfe domin tunkarar duk wani ƙalubale na tattalin arziki

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatinsa na daukar kwararan matakai don farfaɗo da tattalin arzikin Najeriya wanda ya durkushe.

Ya kuma bukaci ƙasashen Afirka su fito su haɗa karfi da ƙarfe su tunkari duk wata gargada da ta tare masu tattalin arziki kuma kada su yi wasa da kowace irin dama.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Babban malami ya cire tsoro, ya buƙaci Shugaba Tinubu ya yi murabus

Bola Ahmed Tinubu.
Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya amince gwamnatinsa na ɗaukar tsauraran matakai domin ceto tattalin arziki Hoto: @OfficialABAT
Asali: Facebook

Shugaba Tinubu ya yi wannan furucin ne ranar Jumu'a a lokacin da ya buɗe taron Afirka na 2204 a Transcorp Hotel da ke Abuja, Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kalaman na Tinubu na zuwa ne bayan fara zanga-zangar nuna adawa da tsare-tsaren gwamnati mai ci a ranar Alhamis da ta wuce.

Tinubu ya ja hankalin ƙasashen Afirka

Tinubu, wanda mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya wakilta, ya ce taron wata dama ce ta yin nazari kan manyan "kalubale da dabarun samar da ci gaba mai dorewa a Afirka".

Ya bukaci kasashen Afirka da su inganta rayuwar jama'a ta hanyar tabbatar da tsarin dimokuradiyya, shugabanci nagari, da bunƙasa tattalin arziƙi.

Dalilin Tinubu na ɗaukar matakai masu tsauri

"A gwamnatance mun bullo da tsare-tsare masu tsauri da nufin ceto tattalin arzikinmu daga koma bayan da aka samu sakamakon matsalolin da suka shafi tattalin arzikin duniya.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban ƙasa ta faɗi wasu manyan ƙusoshin gwamnati da hannu a zanga zanga

"Manufofin da muka zo da su sun mayar da hankali kan dabarun inganta al'amuran kudi, lalubo hanyoyin bunkasa tattalin arziki da samar da ayyukan yi bisa tsarin SDG."

Shugaba Tinubu ya bayyana taron a matsayin wata babbar dama ta musayar tunani, kulla kawance, da kuma tsara hanyar ci gaba cikin haɗin kai, Arise TV ta rahoto.

Zanga-zanga: Uba Sani ya zargi ƴan adawa

A wani labarin kun ji cewa Malam Uba Sani ya zargi wasu ƴan adawa da suka sha kaye a zaɓen 2023 da hannu a zanga-zangar yunwa da ake yi a ƙasar nan

Gwamnan jihar Kaduna ya ce ƴan adawa na amfani da zanga-zangar da zummar ɗaukar fansa kan kashin da suka sha a zaɓe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262