"Arziki da Talauci Duk Na Allah Ne," Gwamna a Arewa Ya Yiwa Masu Zanga Zanga Nasiha

"Arziki da Talauci Duk Na Allah Ne," Gwamna a Arewa Ya Yiwa Masu Zanga Zanga Nasiha

  • Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya buƙaci masu zanga-zanga su tuna cewa Allah ne kaɗai me bayarwa ko hanawa
  • Gwamnan ya kuma nuna takaicinsa kan yadda ɓata gari suka yi amfani da zanga-zanga wajen satar dukiyoyin mutane a Jigawa
  • Jigawa dai na ɗaya daga cikin jihohin da zanga-zangar da aka fara jiya Alhamis ta rikiɗa ta zama tashin hankali da ƙone-ƙone

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jigawa - Gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya tunatar da masu zanga-zangar yunwa a jihar cewa Allah ne kadai ke da ikon talauta ko wadata kowa.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya yi kai tsaye a daren ranar Alhamis, inda ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda zanga-zangar ta koma tashin hankali.

Kara karanta wannan

Rana ta 5: Zanga zanga ta ɗauki sabon salo, wasu matasa sun yi tsirara a kan titi

Gwamna Umar Namadi.
Gwamna Umar Namadi ya ja hankalin masu zanga-zanga kan cewa Allah ne ke bayarwa kuma shi yake hanawa Hoto: Umar Namadi
Asali: Twitter

Gwamnan Jigawa ya ji haushin masu barna

Leadership ta ce Umar Namadi ya nuna takaicinsa kan yadda wasu ɓata-gari suka shiga cikin masu zanga zangar, inda suka riƙa wawushe kayan gwamnati da na al'umma.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit Hausa ta tattaro cewa zanga-zangar da aka fara jiya Alhamis, 1 ga watan Agusta, 2024, kan ƙuncin rayuwa ta samu haɗin kan matasa da dama a sassan ƙasar nan.

Sai dai zanga-zangar ta rikiɗa ta koma tarzoma, sace-sacen barayi da ƙone-ƙone a jihohin Kano, Borno, Kaduna, Gombe, Yobe da Jigawa.

Gwamna Namadi ya tunatar da matasa

Gwamna Namadi ya jaddada cewa ba gwamnati mai ci ce ta kawo wahalhalu da halin ƙuncin da al'umma ke ciki ba.

A rahoton Guardian, Ɗanmodi ya ce:

“A matsayinmu na Musulmai, mun yi imani cewa babu wani mutum a duniya da zai iya sanya mu a wahala sai Allah (SWT), kuma babu wanda zai iya ceto mu daga wani hali sai Shi.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: An kama mutumin da ke ɗinka tutocin ƙasar Rasha a jihar Kano

"Mun fahimci cewa wasu mutane ne suke amfani da matasa domin ɓarnatar da dukiyar mutane da sata, wannan ba addinin mu ba ne kuma ba al'adar mu ba ce."

Nura Abdullahi, wani matashi a Jigawa ya shaidawa Legit Hausa cewa mutane sun harzuƙa da jawabin da Gwamna Namadi ya yi musamman sanya dokar kulle har illa masha Allahu.

A cewarsa, a halin babu da ake ciki galibin mutane sai sun fita suke samun abin da za su ci, to amma an kulle su a gida.

Ya ce:

"Ni ban fita zanga-zanga ba, a farko ina goyon bayan a yi amma da naga ɓarnar da ake yi gaskiya bana goyon baya a yanzu.
"Duk da haka abubuwan da ke faruwa sun nuna cewa talakawa sun kai wuya, za su iya yin komai a yanzu, ya kamata gwamnati ta farka tun kafin lokaci ya ƙure.
"Mu a nan Jigawa an kulle mu saboda sace-sace da ɓarnar masu zanga zanga, wannan matakin ƙara jefa wasu cikin wahala zai yi."

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Duk da barkewar rikici, gwamna ya fadi dalilin kin kulle mutane a guda

Yan sanda sun tarwatsa zanga-zanga

A wani rahoton kuma masu zanga-zanga sun gamu da fushin ƴan sanda yayin da suka sake taruwa a kusa da babban asibitin ƙasa a birnin Abuja.

Matasan sun sake taruwa duk da kashedin da rundunar ƴan sanda ta masu bayan sun tayar da hargitsi a rana ta farko da suka fara zanga-zanga.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262