Rana Ta 2: Rundunar Sojoji Ta Shirya Ɗaukar Mataki Mai Tsauri Kan Masu Zanga Zanga

Rana Ta 2: Rundunar Sojoji Ta Shirya Ɗaukar Mataki Mai Tsauri Kan Masu Zanga Zanga

  • Babban hafsan hafsoshin tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya ce sojoji za su shiga tsakani idan masu zanga zanga suka ci gaba da keta doka
  • Janar Christopher Musa ya bayyana cewa idan suka fahimci lamarin ya sha kan ƴan sanda, za su kawo ɗauki domin tabbatar da zaman lafiya
  • Wannan kalamai na zuwa ne a lokacin da matasan Najeriya suka shiga rana ta 2 a zanga-zangar yunwa da suka fara ranar 1 ga watan Agusta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Rundunar sojojin Najeriya ta ce da yiwuwar ta kawo ɗauki domin murkushe tarzomar da ta taso daga fara zanga-zanga kan tsadar rayuwa.

Babban hafsan hafsoshin tsaron Najeriya Janar Christopher Musa ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai a Abuja ranar Juma’a.

Kara karanta wannan

Rana ta 2: Ƴan sanda sun bude wa masu zanga zanga wuta, mutane da yawa sun jikkata

Sojojin Najeriya.
Sojoji sun bayyana cewa a shirye suke su kawo wa ƴan sanda ɗauki domin magance tarzomar masu zanga-zanga Hoto: @DefenceinfoND
Asali: Twitter

Janar Musa ya bayyana cewa sojoji za su kawo ɗauki idan ƴan sanda suka gaza magance tashin tashinar da ta biyo bayan zanga-zangar, jaridar Punch ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda zanga-zanga ta rikide

Idan ba ku manta ba ƴan Najeriya sun fara zanga-zangar lumana da nufin nuna rashin gamsuwar su da tsare-tsaren gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

A rana ta farko da aka fara wannan zanga-zanga ta riƙiɗe ta koma tashin hankali, ƙone-ƙone da satar kayayyakin gwamnati da na al'umma musamman a jihohin Arewa.

Wane mataki sojoji za su ɗauka?

Amma da yake jawabi ga manema labarai a Abuja, CDS Musa ya ce "sojoji za su shiga" da zarar sun lura cewa lamarin "ya wuce abin da ('yan sanda) za su iya dauka."

Ya yabawa rundunar ‘yan sanda bisa kokarin da take yi na tabbatar da zaman lafiya, ya kara da cewa za a tilastawa sojoji shiga lamarin idan har aka ci gaba da samun tashin hankali.

Kara karanta wannan

Gwamna ya sanya dokar zaman gida ta awanni 24, ya tsara yadda za a yi Sallar Jumu'a

Daily Trust ta rahoto babban hafsan sojin yana cewa:

"Muna kara kashedi ga ɓata-gari, masu kunnen ƙashi cewa ba za mu naɗe hannu muna kallo a rusa ƙasarmu ba. Za mu ɗauki mataki cikin kwarewa. Duk wanda aka kama za a kai shi kotu domin a hukunta shi."

Gwamnan Jigawa ya tunatar da masu zanga-zanga

A wani rahoton kuma Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya buƙaci masu zanga-zanga su tuna cewa Allah ne kaɗai me bayarwa ko hanawa.

Gwamnan ya kuma nuna takaicinsa kan yadda ɓata gari suka yi amfani da zanga-zanga wajen satar dukiyoyin mutane a Jigawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262