Zanga Zanga: Bayan Kaƙaba Dokar kulle, Gwamna Ya Tsara Yadda Za a Yi Sallar Jumu'a
- Gwamnatin Borno ta ɗage dokar hana fita na tsawon awanni uku domin Musulmai su samu damar zuwa masallacin Jumu'a
- Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, Daso Nuhun ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya fitar a Maiduguri
- Gwamnati da hukumomin tsaro sun sa dokar zaman gida ne biyo bayan abubuwan da suka faru a Borno a ƴan kwanakin nan
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Borno - Gwamnatin jihar Borno ƙarƙashin Gwamna Babagana Zulum da hukumomin tsaro ta sassauta dokar hana fita saboda mutane su samu damar zuwa masallacin Jumu'a.
Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar Borno, ASP Daso Nahun ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Jumu'a a Maiduguri.
Ya ce za a sassauta dokar hana fita daga karfe 12:00 zuwa karfe 3:00 na rana domin ba wa musulmi damar zuwa sallar Juma’a a masallatan kusa da su, Punch ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Idan ku na biye dai Legit Hausa ta kawo maku rahoton yadda gwamnatin Borno ta sanya dokar kulle ta sa'o'i 24 sakamakon tashin hankalin da ya biyo bayan zanga-zanga.
Yaushe Borno za ta cire dokar kullen?
Mai magana da yawun ƴan sandan jihar Borno ya bayyana cewa bayan kammala sallar Jumu'a, dokar kullen za ta ci gaba da aiki daga ƙarfe 3:00 na yammacin Jumu'a.
ASP Daso Nuhun ya ƙara da cewa dokar zaman gidan za ta ci gaba da aiki har zuwa ƙarfe 6:00 na yammacin gobe Asabar, 3 ga watan Agusta, 2024.
Nahun ya bai wa jama’a tabbacin kare rayuka da dukiyoyinsu, tare da kokarin tabbatar da dorewar zaman lafiya da tsaro a jihar.
Wane mataki gwamnatin Borno ta ɗauka?
"An ɗauki wannan mataki biyo bayan wasu abubuwa da suka faru a jihar, ciki har da zanga-zanga, fashewar bama-bamai, da kuma kisan kai.
"Gwamnati da hukumomin tsaro suna aiki ba kama hannun yaro don tabbatar da doka da oda tare da tabbatar da tsaron lafiyar jama’a,” inji shi.
Gwamnan Jigawa ya bada lokacin Jumu'a
A wani rahoton kuma Gwamna Umar Namadi ya sanar da sanya dokar hana fita ta tsawon awanni 24 a Jigawa bayan tashe tashen hankulan da suka faru.
Ɗanmodi ya bayyana cewa za a sassauta dokar daga karfe 12:00 zuwa 2:30 na rana domin ba mutane damar zuwa Masallacin Jumu'a.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng