Rana Ta 2: Masu Zanga Zanga Sun Sake Fitowa a Abuja, Sun Gamu da Fushin Ƴan Sanda

Rana Ta 2: Masu Zanga Zanga Sun Sake Fitowa a Abuja, Sun Gamu da Fushin Ƴan Sanda

  • Masu zanga zanga sun kara fitowa a rana ta biyu, sun taru a babban shataletalen Berger da ke babban birnin tarayya Abuja ranar Jumu'a
  • Ƴan sanda sun dura wurin kuma sun tarwatsa masu zanga-zangar da hayaƙi mai sa hawaye, sun haɗa da ƴan jaridar da ke wurin
  • Wannan na zuwa ne sa'o'i 24 bayan ƴan Najeriya sun ɓarke da zanga-zanga kan yunwar da ake fama da ita

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Jami'an ƴan sanda sun harba barkonon tsohuwa mai sa hawaye kan masu zanga-zangar da suka sake taruwa a babban shataletalen Berger da ke Abuja.

Su kansu ƴan jarida da ke ɗaukar rahoton abubuwan da ke faruwa ba su tsira ba domin ƴan sandan sun fesa masu hayaki mai sa hawaye a wurin da suka taru a gefe ɗaya.

Kara karanta wannan

Rana ta 2: Ƴan sanda sun bude wa masu zanga zanga wuta, mutane da yawa sun jikkata

Yan sandan Najeriya.
Yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga a rana ta 2 a Abuja Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Abuja: Ƴan sanda sun kori ƴan jarida

Wakilin Channels tv da ke wurin ya bayyana cewa ƴan sanda sun tarwatsa masu zanga-zangar da hayaƙi mai sa hawaye, su kansu ƴan jarida ba su tsira ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu masu wucewa da masu ababen hawa sun soki ƴan sanda bisa harba barkonon tsohuwar wanda ya rutsa da su a wurin.

Wannan dai na zuwa ne bayan ƴan Najeriya galibi matasa sun fara zanga-zangar adawa da manufofin gwamnati mai ci waɗanda suka kawo tsadar kayayyaki.

Matasan sun fara zanga-zangar jiya Alhamis, 1 ga watan Agusta, 2024 a mafi yawan jihohin Najeriya da babban birnin tarayya Abuja, Vanguard ta tattaro.

Masu zanga-zanga sun sake fitowa a Abuja

A yau Jumu'a, 2 ga watan Agusta, 2024 masu zanga-zangar sun sake fitowa a Abuja, inda aka ji suna maimaita, "Akwai yunwa a kasa," "akwai yunwa a ƙasa."

Kara karanta wannan

Masu zanga zanga sun dira gidan Buhari a Daura, bayanai sun fito daga Katsina

Sai dai jim kaɗan bayan haka wasu dakarun ƴan sanda suka tarwatsa su a shataletalen Berger da ke babban birnin tarayya.

Malamin addini ya bukaci Tinubu ya sauka

A wani rahoton kuma wani babban malamin addini ya buƙaci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi murabus idan ba zai iya gyara tattalin arziki ba.

Farfesa Princewilll Ariwodor ya ce Buhari ya miƙa tattalin arziki mai kyau ga Tinubu amma ya lalata shi da tsare-tsaren da ya zo da su.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262