IGP Ya Umarci Ƴan Sanda Su Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Abubuwa 2 a Lokacin Zanga Zanga
- Babban sufetan ƴan sanda na kasa ya ɗauki zafi kan masu yunƙurin ta da zaune tsaye da ƙone-ƙone a lokacin zanga-zangar da za a yi
- IGP Kayode Egbetokun ya umarci ƴan sanda su ɗauki mataki mai tsauri kan duk wanda suka kama da aikata laifi a faɗin kasar nan
- Sufeta Janar ya bayyana cewa sun samu bayanan sirri na shirin da wasu gurɓatattu ke yi kuma ya tabbatar da cewa za su ɗauki mataki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Babban sufetan ƴan sanda na ƙasa, Kayode Egbetokun, ya umarci jami'ai su ɗauki tsattsauran mataki kan masu ƙone-ƙone da tada zaune tsaye a lokacin zanga-zanga.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da IGP Kayode ya sa wa hannu da kansa gabanin fara zanga-zangar gama gari kan tsadar rayuwa a Najeriya.
IGP Kayode ya soki masu shirya zanga-zanga
Shugaban ‘yan sandan ya ce wadanda suka shirya zanga-zangar sun kasa ba ‘yan sanda cikakken bayanin kan yadda za ta gudana, Channels tv ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
IGP ya ce sunan da aka ba kungiyar 'Take It Back Movement' yana ƙunshe da ma'anar da ta saɓa tsarin dimokradiyya da kundin tsarin mulkin ƙasar nan
Ya bayyana cewa bayanan sirri da suka samu sun nuna cewa ana shirin tayar da tarzoma da farmakar waɗanda babu ruwansu a lokacin wannan zanga zanga.
Egbetokun ya ce 'yan sanda ba za su nade hannayensu ba su zuba ido suna kallo wasu marasa kishi su tayar da hankulan al'umma, rahoton Daily Post.
Sufeta Janar ya ba ƴan sanda umarni
Sakamakon haka ya umarci duka dakarun ƴan sanda a faɗin kasar nan su zauna cikin shiri domin kare rayuka da dukiyoyin ƴan Najeriya.
"Mun umarci dukkan jami’an ‘yan sandan Najeriya su dauki mataki mai tsauri kan masu kone-kone, tsoratarwa ko musgunawa wani dan kasa da masu barazana ga rayuka da dukiyoyi.
"Da duk masu yunkuri ruguza zaman lafiya da sauran manyan laifukan da aka iya tasowa a lokacin zanga-zangar da za a yi, mun ba yan sanda umarnin su ɗauki mataki.
"Za a kama duk wadanda suka aikata kowane irin laifi kuma a gurfanar da su a gaban ƙuliya" in ji shi.
Da gaske an ɗage zanga-zanga?
A wani rahoton kuma, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar AAC, Omoyele Sowore ya musanta rahoton ɗaga zanga-zangar yunwa da za a fara.
Sowore ya bayyana sanarwar da ke yawo cewa an sauya tsarin zanga-zangar a matsayin ƙarya mara tushe balle makama.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng