Yan Sanda Sun Tono Wani 'Bom' da Aka Dasa Kwana 1 Gabanin Fara Zanga Zanga

Yan Sanda Sun Tono Wani 'Bom' da Aka Dasa Kwana 1 Gabanin Fara Zanga Zanga

  • Yan sanda sun yi nasarar kwance bom a jaka a yankin Ikeja da ke jihar Legas a shiyyar Kudu maso Yammacin Najeriya
  • Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Legas, Benjamin Hundeyin, ya ce wani mutum a mota mara lamba ne ya jefar da bom din ranar Laraba
  • Wannan lamari na zuwa ne yayin da ya rage awanni gabanin ƴan Najeriya su fara zanga-zanga kan tsadar rayuwa da yunwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Lagos - Rundunar ƴan sanda reshen jihar Legas ta gano wani 'bom' da aka dasa a katangar FOU, Zone A da ke Bank Anthony way a Ikeja yau Laraba.

Rundunar ta ce tuni jami'an ƴan sanda na sashen kwance bom suka yi nasarar warware bom ɗin da aka gano lami lafiya.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya fito fili ya goyi bayan zanga zanga, ya caccaki 'yan sanda

Yan sandan Najeriya.
Yan sanda sun kwance wani 'bom' da aka ajiye a gefen titi a jihar Legas Hoto: @PoliceNG
Asali: Getty Images

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin ne ya tabbatar da lamarin ga jaridar Punch ranar Laraba, 31 ga watan Yuli, 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce sun gano cewa wata mota mara lambar rijista ce ta jefar da bom ɗin wanda ke nannade a cikin jaka, a gefen hanyar Bank Anthony Way.

Ana dab da fara zanga-zanga

Daily Trust ta ruwaito cewa an gano wannan bom ne a jajibirin gudanar da zanga-zangar adawa da wahalhalu da tsadar rayuwar da ake ciki a fadin kasar nan.

Zanga-zangar ta tsawon kwanaki 10 za ta fara ne daga ranar 1 ga Agusta kuma za ta kare a ranar 10 ga Agusta, 2024, a cewar waɗanda suka shirya.

Yadda ƴan sanda suka kwance bom

An tattaro cewa wani mutumi da ba san ko wanene ba a cikin mota mara lamba ya ajiye jakar bom ɗin, sannan ya bar wurin cikin kankanin lokaci.

Kara karanta wannan

Ana saura kwana 1, gwamnatin Tinubu ta aike da muhimmin saƙo kan zanga zanga

Da yake jawabi kan lamarin, kakakin ƴan sanda ya ce wani jami'an rundunar kwance bama-bamai EOD ne ya fara ganin wanda ake zargin ya jefar da jakar bom ɗin.

"Bayan tabbatar da rahoton rundunar EOD, nan take jami'an ƴan sanda suka mamaye wurin kuma suka tabbatar da cewa bom ne a jakar, daga bisani suka kwance shi."

Tsohon gwamna ya caccaki ƴan Arewa

A wani rahoton kuma Ayodele Fayose ya soki wasu ƴan Arewa da suke yawan haihuwa ba tare da suna samun isassun kudin kulawa da ƴaƴansu ba.

Tsohon gwamnan jihar Ekiti ya bayyana cewa hakan karawa gwamnati nauyi ne wadda a yanzu take kokarin tsayawa da kafafunta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262