Gwamna Abba Ya Ɗauki Mataki Kan Masu Zanga Zanga a Kano, Ya Aika Masu Goron Gayyata
- Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya gana da malamai, sarakuna da ƴan kasuwa a gidan gwamnati kan zanga-zangar da za a fara
- Gwamma Abba ya ce gwamnatinsa ba za ta lamunci duk wani abin da zai tada hankula ba a lokacin zanga zanga
- Ya kuma gayyaci masu shirin yin zanga-zangar domin su zo gidan gwamnatin Kano su tattauna kan kokensu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya ce gwamnati ba za ta lamunci wani yunkuri ba zai kawo tashin hankali ba a zanga-zangar da za a yi gobe Alhamis.
Abba Kabir ya faɗi haka ne a lokacin da yake jawabi ga ’yan kasuwa, sarakunan gargajiya, da malaman addini a gidan gwamnati da ke Kano yau Laraba.
Gwamna ya jaddada cewa zanga-zanga ba za ta kai mutane ko'in ba, bisahaƙa ya ja kunnen matasa su guje wa tada zaune tsaye, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kuma ƙara da rokon masu shirin yin amfani da ‘yancinsu na fitowa zanga-zanga da su kaucewa duk wani hali da ɓata gari za su yi amfani da shi wajen tayar da tarzoma.
Gwamnan Abba ya gayyaci masu zanga-zanga
"Mun samu sahihan bayanan sirri cewa wasu daiɗaikun mutane sun ɗauko hayar ƴan daba domin tada fitina a jihar Kano. Ina tabbatar muku da cewa gwamnati ba za ta lamunci haka ba.
"A maimakon haka, ina mika goron gayyata ga masu son gudanar da zanga-zanga da su zo gidan gwamnati, inda zan ji dadin sauraren koke-kokensu, sannan mu tattauna da su."
- Abba Kabir Yusuf.
Gwamna ya ambaci wasu tsare-tsaren da gwamnatinsa ta kawo na inganta rayuwar al'umma da kuma tsamo su daga halin wahalar da ake ciki.
Gwamnatin Tinubu ya roki ƴan Najeriya
A wani rahoton kuma Sakataren gwamnatin tarayya, George Akume ya roƙi ƴan Najeriya sun gujewa zanga zangar da aka shirya yi a watan Agusta.
Sanata Akume ya tabbatar wa al'umma cewa wannan wahalar da ake ciki ba za ta dawwama ba, nan gaba kaɗan za a ji daɗi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng