Sarki Mai Shekara 102 Ya Riga Mu Gidan Gaskiya, Ya Rasu Bayan Shekara 47 a Mulki

Sarki Mai Shekara 102 Ya Riga Mu Gidan Gaskiya, Ya Rasu Bayan Shekara 47 a Mulki

  • Sarki mai daraja ta farko a jihar Ondo, Owa na masarautar Idanre Oba Frederick Adegunle Aroloye, ya riga mu gidan gaskiya
  • Fadar sarkin ta bayyana cewa Oba Aroloye ya rasu ne da safiyar ranar Laraba, 31ga watan Yuli, 2024 yana da shekara 102 a duniya
  • Idanre yana daya daga cikin wuraren UNESCO a duniya, gari ne da ke kewaye da tsaunuka, yana da matakala sama da 600

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ondo - Owa na masarautar Indanre, Oba Frederick Adegunle Aroloye (Arubiefin na IV) ya riga mu gidan gaskiya yana da shekara 102 a duniya.

Oba Aroloye shi ne sarki mai daraja ta farko a kasar Idanre da ke jihar Ondo a Kudu maso yammacin Najeriya.

Kara karanta wannan

MTN sun rufe maka layi? Ga wata hanya mai sauki ta bude layukan da aka rufe

Owa na Idanre, Oba Aroloye.
Wani sarki a jihar Ondo, Owa na Idanre ya riga mu gidan gaskiya Hoto: @OlofinsaweAkin1
Asali: Twitter

Sarki Aroloye mai shekara 102 ya rasu

Cif Christopher Oluwole Akindolire ne ya tabbatar da rasuwar, inda ya bayyana cewa sarkin ya cika ne da safiyar yau Laraba, 31 ga watan Yuli, 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotan TVC News ya nuna cewa tuni aka fara bukukuwan jana'iza na al'ada a masarauta domin girmama basaraken bayan Allah ya karɓi rayuwarsa.

Yaushe Oba Aroloye ya zama Sarki?

Oba Aroloye ya dade yana sarauta, inda ya hau karagar mulki a shekarar 1976 watau ya shafe sama da shekaru 45 yana kan mulki.

An tattaro cewa zai yi wahala mutanen yankin masarautar su manta da kyawawan ayyukan da basaraken ya yi a lokacin rayuwarsa, rahoton Daily Trust.

Taƙaitaccen bayani kan kasar Idanre

Idanre gari ne mai cike da tarihi da ke cikin jihar Ondo a Najeriya. Yana da tazarar kilomita 24 daga Kudu maso Yammacin Akure, babban birnin jihar.

Kara karanta wannan

Rai bakon duniya: Tsohon kwamishina a Kaduna ya kwanta dama

Garin yana cikin wani kwari da ke kewaye da manyan tsaunuka, wanda ya sa ake yi masa lakabi da "tsohon birnin tsaunuka."

Idanre yana cike da kyawawan al'adun gargajiya kuma ana kiransa da gidan tsaunin Idanre, ɗaya daga cikin yankunan kungiyar UNESCO ta Duniya.

An buƙaci gwamna ya hukunta wasu sarakuna

A wani labarin kuma matasa a jihar Ondo sun bukaci Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya hukunta wasu daga cikin sarakunan da ke mulki.

Kungiyar matasan da ake kira da Indigenous Youth Leaders ta bukaci gwamnan ya hukunta sarakuna da ke daurewa masu aikata laifuka gindi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262