Mutanen Kano Sun Shiga Sabuwar Matsala Kwana 1 Gabanin Fara Zanga Zanga
- Yayin da ake shirin fara zanga-zanga, mazauna Kano sun koka kan rashin karfin intanet da tangarɗa wajen kiran waya
- A hira daban-daban da aka yi da mazauna birnin Kano musamman ƴan kasuwa sun nuna yadda tankarɗar sadarwa ta jefa su cikin yanayi
- Wata malamar makaranta, Maryam Adamu ta yi kira ga kamfanonin sadarwa su ƙara ƙaimi wajen inganta ayyukansu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Mazauna Kano musamman masu amfani da layukan manyan kamfanonin sadarwa sun koka kan rashin karfin intanet da kiran waya a cikin birni.
Hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) a ranar Talata ta tattaro cewa rashin ƙarfin sadarwa ya jefa mutane da dama musamman ƴan kasuwa cikin ƙunci.
Ƴan kasuwa a jihar Kano sun koka
Kamar yadda jaridar Punch ta tattaro, ɗan kasuwar ya zargi kamfanonin sadarwa na ƙasar nan da cewa ba su damu da biyan buƙatun kwatomomin su ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani dan kasuwa Abubakar Isah, ya ce a ƴan kwanakin nan suna samun matsala a hanyoyin sadarwa, katsewar intanet da tangarɗar kiran waya a kwaryar birnin Kano.
Abubakar wanda ya yabawa hukumar sadarwa ta ƙasa (NCC) bisa ƙoƙarin da take yi, ya buƙaci ta ƙara kaimi wajen kare hakkokin masu amfani da layukan sadarwa.
Wani mai shagon yanar gizo, Ahmad Nuhu ya bayyana cewa hanyoyin sadarwa sun samu tangarɗa a ƴan kwanakin nan, wanda ya kawo cikas ga kasuwancin su.
Sai dai ya yi kira ga hukumomi su shiga cikin lamarin kana su ceto ƴan Najeriya daga abin da ya kira zaluncin kamfanonin sadarwa, rahoton Gazettengr.
Ƴan Najeirya sun fara zuwa wuya
Haka nan kuma wata malamar makaranta, Maryam Adamu, ta bukaci kamfanonin sadarwa da su inganta ayyukansu saboda ‘yan Najeriya sun fara fusata da su.
Maryam, wanda ta yi zargin kamfanonin sun fi damuwa da ribar da suke samu, ta buƙaci su kara kaimi wajen ɓullo da tsare-tsaren da za su inganta ayyukansu.
Ta kuma koka da yadda aka rufe ofishin MTN da ke cikin birni inda ta je domin a buɗe mata layinta da aka rufe.
Kabiru Suleiman, wani tela a Kano ya shaidawa wakilin Legit Hausa cewa shi da abin ya ba shi haushi ajiye wayar ya yi a gida.
"Gaskiya muna fama da matsalar sabis, ni babban abin da ya fi damu na shi ne hana mu kiran waya, musamman MTN, ni daga ƙarshe ma aje wayar na yi don ba ta da amfani.
"Ya kamata gwamnati ta tsawatar wa kamfanonin sadarwa, barin su suna yin abin da suka ga dama shi ke kawo irin haka, ya kamata su gyara," in ji shi.
Zanga-zanga ta samu koma baya
A wani rahoton na daban matasan Najeriya sun kara gamuwa da cikas game da shirinsu na fara zanga-zangar adawa da manufofin gwamnati da suka jawo tsadar rayuwa.
Kungiyoyi da dama a Arewacin Najeriya sun sanar da janyewa daga zanga-zangar ranar Litinin saboda abin da suka alaƙanta da barazanar tsaro.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng