Rundunar Ƴan Sanda Ta Yi Wa Matasa Gata Kwanaki 3 Gabanin Fara Zanga Zanga
- Sufetan ƴan sanda na ƙasa, IGP Kayode Egbetokun, ya umarci a tabbatar da tsaron duk wanda ya fito zanga zangar da za a yi a watan Agusta
- Hakan na kunshe a wata takardar amsa da shugaban ƴan sandan ya aika ga babban lauya mai kare hakkin ɗan adam, Ebun-Olu Adegboruwa
- Daga ranar 1 zuwa 10 ga watan Agusta ƴan Najeriya suka tsara gudanar da zanga-zanga kan tsadar rayuwa da wahalhalun manufofin Tinubu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Babban Sufeto Janar na ‘yan sanda (IGP), Kayode Egbetokun, ya umurci manyan jami’an ‘yan sanda su tabbatar da tsaron masu shirin yin zanga-zanga a faɗin ƙasar nan.
Ƴan Najeriya mafi akasari matasa sun shirya gudanar da zanga-zanga kan tsadar rayuwa daga ranar 1 zuwa 10 ga watan Agusta, 2023.
A wata takarda da IGP ya aika ga lauya, Ebun-Olu Adegboruwa, ya umarci ƴan sanda su bayar da kariya ga duk wanda ya fito wannan zanga zanga, Channels tv ta kawo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zanga-zanga: Lauya ya nemi tsaro daga IGP
Tun farko dai babban lauyan mai fafutukar kare hakkin ɗan adam, Adegboruwa (SAN) ya rubuta wasika zuwa ga sufetan ƴan sandan, inda ya nemi a ba masu zanga-zanga tsaro.
Lauyan ya rubuta wasiƙar zuwa ga IGP ne a madadin kungiyar Take It Back Movement, ɗaya daga cikin kungiyoyin da za su shiga zanga-zangar a watan Agusta.
IGP ya karɓi bukatar masu zanga-zanga
A wasikar amsa ga lauyan mai dauke da kwanan wata 29 ga Yuli, 2024, sufetan ƴan sanda na ƙasa ya umurci manyan jami’an ‘yan sanda samar da tsaro da kariya ga matasa.
IGP ya kuma bukaci ganawa da Adegboruwa a Abuja a ranar Talata, 30 ga watan Yuli, 2024, domin tattaunawa kan bukatarsa, kamar yadda The Nation ta rahoto.
Takardar martanin IGP kayode na ɗauke da sa hannun shugaban ma'aikatan ofishin babban sufetan ƴan sanda, CP Johnson Adenola.
"Ina mai sanar da kai cewa sufeta janar na ƴan sanda ya bayar da umarnin a saurari buƙatarka (ta samar da tsaro ga masu shirin zsnga zanga."
NSCDC ta gano tuggu a zanga-zanga
A wani labarin kuma Hukumar tsaron farar hula (NSCDC) ta ce ta gano wani shiri na 'yan ta'adda da suke son mamaye zanga-zangar da ake shirin yi
Babban kwamandan NSCDC, Abubakar Ahmed Audi ya ce manufar 'yan ta'addan ita ce lalata kadarorin gwamnati yayin zanga-zangar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng